2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa
- Hamisu Chidari, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, ya ce jam'iyyar APC a jihar za ta goyi bayan burin Tinubu
- Chidari ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba, yayin kaddamar da kungiyar tallafawa Tinubu (TSG) ta siyasa a Abuja
- A cewarsa, jihar za ta mayar da goyon bayan da Tinubu ya bai wa Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa a 2015
Biyo bayan jita-jitar burin takarar shugaban kasa na jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Hamisu Chidari, yayi babbar magana.
Legit.ng ta rahoto cewa ya ce APC a jihar Kano za ta goyi bayan Tinubu idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Chidari ya yi magana ne a wajen kaddamar da kungiyar goyon bayan Tinubu (TSG) da kwamitocin gudanarwa na kungiyar a Abuja ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba.
Ya ce jihar Kano, wacce ke da mafi yawan masu jefa kuri’a da wakilai a kasar, za ta rama alherin Tinubu na taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a 2015.
A cewarsa:
"Manufata ita ce fara tafiya wacce za ta kai mu Villa da yardar Allah tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan Najeriya na daya.
“A Kano, kasancewar jihar da ke da mafi yawan wakilai, mun riga mun yanke shawara kuma mun kammala; muna shirin ba shi akalla 98% na wakilai a zaben fidda gwani.
"Ba wannan kadai ba, a shirye muke don ba shi mafi yawan kuri'u don haka zuwa 29 ga Mayu, 2023, za mu kasance a Eagle Square don rantsar da shi a matsayin shugaban kasa."
Da yake magana kamar wannan, dan majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin kudi, James Faleke, ya ce Tinubu ya yaki cin hanci da rashawa ta hanyar amfani da fasaha yayin da yake gwamnan jihar Legas.
Faleke, wanda yayi magana yayin kaddamar da kungiyar goyon bayan, yace:
“Mafi karancin sadaukarwa da za mu iya yi shi ne mu bar kasa baki daya ta ga shugabancin da muka gani, ta ji tausayawar da muka ji, sannan mu sanya maginin Legas zuwa ta zamani ya zama mai kawo gyara ga uwa Najeriya.
“Maganar da na yi cewa Asiwaju Bola Tinubu shi ne ya kirkiro Jihar Legas ta zamani, magana ce ta gaskiya. Yanayin shimfidar wurin na iya ba da labarin canjin da aka samu daga 1999 zuwa 2007.”
Ni ne zan iya gyara Najeriya: Atiku ya bayyana irin kwarewarsa a shugabanci
A bangare guda, Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce Najeriya na bukatar shugabanci wanda zai gyara tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya.
Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba a Abuja yayin gabatar da lacca na cika shekaru 70 da gabatar da littafin Shugaban Kamfanin DAAR Communications Plc, Cif Raymond Dokpesi.
Ya kara da cewa kasar na kuma bukatar jagora wanda zai hada kai, sake fasali da tabbatar da tsaron 'yan kasar.
Asali: Legit.ng