Duk da alheran da na yi wa Ganduje sai ga shi nine babban abokin adawar sa - Kwankwaso

Duk da alheran da na yi wa Ganduje sai ga shi nine babban abokin adawar sa - Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya magantu kan alakarsa da Gwamna Abdullahi Ganduje
  • Kwankwaso ya bayyana cewa bai ga sakon murnar zagayowar ranar haihuwa da gwamnan na Kano ya aika masa ba saboda ayyuka sun yi masa yawa
  • Shugaban na kwankwasiyya ya kuma ce ya zauna lafiya da Ganduje amma sai ga shi ya zama shine babban makiyin sa

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi tsokaci a kan yadda alaka take tsakaninsa da magajinsa, Dr Abdullahi Umar Ganduje kafin tayi tsami.

A yayin hirarsa da sashin Hausa na BBC, Kwankwaso ya bayyana cewa ya zauna lafiya kuma da zuciya daya da tsohon aminin nasa.

Duk da alheran da na yi wa Ganduje sai ga shi nine babban abokin adawar sa - Kwankwaso
Duk da alheran da na yi wa Ganduje sai ga shi nine babban abokin adawar sa - Kwankwaso Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da aka tambaye shi kan ko ya yi mamaki da sakon taya murnar cika shekaru 65 da Ganduje ya aika masa, Kwankwaso ya ce:

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shayen kwayoyi a jihar Kano

“Gaskiya toh in yau yayi ina ta aikace-aikace ban sani ba. Ka ga ai wannan inda tun farko ma haka yake yi yana abubuwa, ai duk mutumin da yake shekara hudu da nayi a nan shine mataimakina. Duk wanda ya san ni duk wanda muka yi aiki da shi babu wanda zai ce ya zo ya fadi zancen Ganduje ko ya fadi laifinsa ma na saurare shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Su dukkaninsu ma sun sani kwamishinonin, sauran manya, ma’aikata da mutan gari, saboda kowa yana da laifinsa, idan ka ce mutum laifi a ciki yana da daya yana kuma da rashin laifi tara, toh idan ka ce z aka kalle shi da wannan laifi guda daya, ai ka ga akwai matsala.
“Saboda haka mun zauna da mutane lafiya har da shi, haka muka bar gwamnati, haka muka tafi hukumar tsaro da shi, haka muka kare ya tafi can Chadi, haka kuma yana can nace ka zo ka yi murabus a gida, ka zo muyi aiki da kai. Na dauki fom na mataimakin gwamna na ba shi, aka gama nace kai ne babba ungo ga baki daya, ba tare da naira daya ba saboda mu a tsarinmu na Kwankwasiyya babu wanda ake cewa ya kawo ko sisin kwabo.”

Kara karanta wannan

Ba zama: Wani mutum ya yi garkuwa da dan sufeton 'yan sanda

Sai dai kuma ya ce duk da tarin alheran da yayi masa, da tafiya tayi tafiya sai gashi Ganduje ya yi masa butulci domin bai da babban abokin adawa sama da shi.

Rabiu Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shayen kwayoyin farko a Najeriya

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shaye.

Legit.ng Hausa ta samu labari Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da Amana Sanatorium, domin gyaran halin wadanda suka fada wa shan kwayoyi.

Punch tace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zuba kayan aiki a wannan asibiti da aka bude. Akwai sashen kula da wadanda takaici ya yi masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng