Tsohon Shugaban Majalisa ya rubuta littafi, ya tona asirin Obasanjo na neman zarcewa a mulki

Tsohon Shugaban Majalisa ya rubuta littafi, ya tona asirin Obasanjo na neman zarcewa a mulki

  • Ken Nnamani ya wallafa littafi a game da yunkurin tazarcen da aka yi a 2007
  • Nnamdi yace Olusegun Obasanjo ya nemi ya cigaba da mulki bayan wa’adinsa
  • Olusegun Obasanjo yana musanya zargin cewa ya so ya cigaba da zama a ofis

Abuja - Punch tace tsohon Ministan tsaro kuma babban sojan Najeriya, Janar Theophilus Y. Danjuma ya yabi litaffin ‘Standing Strong’ da Ken Nnamani ya rubuta.

Sanata Ken Nnamani ya rubuta wannnan litaffi na ‘Standing Strong’ domin ya yi bayanin irin yunkurin da Olusegun Obasanjo ya yi na tsawaita wa’adinsa a kan mulki.

Janar Theophilus Danjuma wanda ya yi aiki da Obasanjo a lokacin da ya yi mulki a 1999 da zamanin soja tsakanin 1976 da 1979, shi ne wanda ya kaddamar da littafin.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda Ministan Buhari yake amfani da kujerarsa yana yin abin da ya ga dama a mulki

An kaddamar da wannan litaffi da Theophilus Danjuma ya kira tarihi mai ban kaye a ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2021 a babban birnin tarayya da ke Abuja.

A wajen bikin da aka yi, Danjuma ya taya Ken Nnamani murnar rubuta wannan littafi, yace ya tattaro tarihin kasar nan a lokacin da ba a wani san darajar adana tarihi ba.

Tsohon Shugaban Majalisa
Sanata Ken Nnamani Hoto; authorityngr.com
Asali: UGC

Tsohon sojan yake cewa a halin yanzu mutane sun fi sha’awar yamadidi da labaran karya a Najeriya.

“Saboda haka ina so in fada maku cewa ko da kun manta komai yau da safen nan, ka da ku manta an tattara abubuwan da suka faru, kuma kowa ya mallaki littafin.”

An rahoto Janar Danjuma yana kira ga jama’a su samu wannan littafi na ‘Standing Strong’ watau tsaya wa tsayin-daka domin su shaida abubuwan da suka rika wakana.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

A jawabinsa, Mai girma Muhammadu Buhari ya yabi irin kokarin Sanata Ken Nnamani wanda yanzu jagora ne a jam’iyyar APC, yace ya ceci damukaradiyyar Najeriya.

Ministan kimiyya fasaha da kirkire-kirkire na kasa, Dr. Onu ne ya wakilci shugaban kasa wajen taron kaddamar da litaffin, ya kuma yabi sauran ‘yan majalisa na lokacin.

Rahoton yace Mataimakin shugaban kasa Farfesa, Yemi Osinbajo ya samu halartar wannan taro.

A Kano kun ji cewa yayin da ake tsakiyar rigingimu a APC, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tura sakon taya murnar cika shekara 65 ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ganduje ya aika wa tsohon Mai gidansa Kwankwaso sakon taya shi murnar cika shekara 65.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng