Rikicin Shugabancin APC a Kano: Shekarau ya bayyana matakin shi da magoya bayansa suka ɗauka
- Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Kano ya yi bayani game da matsayinsa da magoya bayansa a APC na Kano
- Shekarau ya bayyana cewa ya shigar da korafi a hedkwatar jam'iyya na kasa kan rashin gamsuwa da zaben shugabannin jam'iyyar
- Sardaunan na Kano ya ce ba zai fice daga APC ba amma ba zai saurari kowa ba sai wadanda ya kai wa korafi a hedkwatar jam'iyya
Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, a ranar Laraba ya ce bangarensa ba za ta amince da wasu sabbin shugabanni da aka zaba ba yayin gangamin zaben jam'iyyar APC a ranar Asabar.
'Yan siyasa da ke yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano biyayya ne suka hallarci taron.
Shekarau, wanda shine sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya da wasu takwarorinsa daga majalisar tarayya sun yi nasu gangamin amma uwar jam'iyyar APC bata yi na'am da shi ba.
Hakan yasa Shekarau da sauran wadanda abin bai musu dadi ba suka shigar da korafi a hedkwatar jam'iyyar na kasa don nuna rashin gamsuwarsu kan yadda aka yi zabuka a mazabu da kananan hukumomi kafin gangamin jihar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shekarau ya ce shi da magoya bayansa ba su yi na'am da zaben da aka yi ba yana mai cewa an ware su a gefe guda.
Wani sashi na rubutunsa na cewa:
"Ni Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci wasu daga cikin wadanda aka zabe mu, daga majalisar kasa. Mun shigar da kuka ga uwar jam'iyya akan rashin gudanar da abubuwan da suka shafi jam'iyya tare da damu. Mu zababbu ne, jama'armu suna da hakki. An karbi korafinmu da mutumtawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana.
"Ina sanar da duk jama'armu, ina cikin jam'iyyar APC daram-dam, zamu tsaya har illa Masha Allahu. A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba zamu lamunci sakarci ba. Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba zamu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka."
Shekarau ya sake jadada cewa su a wurinsu a jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shine zababben shugaban APC na jiha da sauran mutum 35 da aka zaba tare da shi.
Amma a bangaren gwamna Ganduje kuma Abdullahi Abbas ne aka zaba a matsayin shugaban jam'iyyar na APC a Kano.
Asali: Legit.ng