Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar APC
  • Sanata Shekarau yace ba zai yuwu ya zura ido yana kallo wasu na tafiyar da APC a matakin jiha ba tare da su ba, bayan zaban su al'umma suka yi
  • Yace tuni tsaginsa ya aike da korafi ga uwar jam'iyya ta ƙasa, kuma babu wanda zasu saurara sai mahukunta

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahin Shekarau, ya bayyana cewa yana nan daram a cikin jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan, wanda a halin yanzun yake wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, yace ba gudu ba ja da baya kan sabon shugaban APC na Kano, Ahmadu Haruna Danzago.

Sanata Shekarau ya faɗi haka ne a wani rubutu da ya buga a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

Malam Shekarau
Siyasar Kano: Ba inda zanje, Ina nan daram a jam'iyyar APC, Tsohon Gwamnan Kano ya maida Martani Hoto: @Malam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Shekarau yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina son amfani da wannan damar wajen sanar da abokai da yan uwa halin da jam'iyyar APC take ciki a jihar Kano."
"Ni, Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci mambobin majalisar tarayya mun kai ƙorafi sakateriyar APC ta ƙasa kan yadda ake tafiyar da jam'iyya ba tare da mu ba."
"Zaɓar mu aka yi, kuma mutane suna da damar sanin abubuwan dake tafiya a cikin jam'iyya, an karbi korafinmu da mutuntawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana."

Waye shugaban APC reshen Kano?

Sanata Shekarau ya ƙara da cewa babu wanda ya sani a matsayin shugaban APC reshen jihar Kano sai Ahmadu Haruna Danzago.

"A jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam'iyyar APC zababbe a gurinmu. Muna yi masa addu'ar Allah ya karfafi zuciyarsa kuma Allah ya taya shi riko."

Kara karanta wannan

2023: Mun shirya tsaf don yin kaca-kaca da APC a Zamfara, mataimakin gwamna

Ina nan daram a cikin APC - Shekarau

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa yana nan daram a cikin jam'iyyar APC kuma ba ya fatan fita amma ba zai yarda da wulaƙanci da sakarci ba.

"Ina mai sanar da duk jama'armu cewa, ina cikin jam'iyyar APC daram-dam, zamu tsaya har inda Allah ya so."
"A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba zamu lamunci sakarci ba."
Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba zamu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka."

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya.

Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262