Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa zasu ɗauki matakin sulhu da tsagin Malam Shekarau
  • Ganduje wanda ya ƙara jaddada cewa APC ta ƙasa Abdullahi Abbas ta sani a matsayin shugaba na Kano, yace siyasa ta gaji sulhu
  • Rikicin APC a Kano ya ƙara fitowa fili ne bayan zabar shugabanni biyu daga ɓangare biyu na Ganduje da Shekarau

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, yace tuni aka fara kokarin sulhu tsakaninsa da tsagin jam'iyyar APC ƙarƙashin Malam Shekarau.

Dailytrust ta ruwaito cewa jami'iyyar APC ta tsage gida biyu a jihar Kano, inda shugabannin jam'iyya guda biyu suka bayyana bayan taron gangami na jiha.

Sai dai gwamna Ganduje ya ƙara jaddada cewa uwar jam'iyya ta ƙasa ta amince da shugaban APC na jihar Kano, wanda ya fito daga tsaginsa, Abdullahi Abbas.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

Ganduje da Shekarau
Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Dama siyasa ta gaji sulhu - Ganduje

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan, Abba Anwar, ya fitar, jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa, Ganduje yace, "siyasa ta gaji sulhu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika gwamnan ya yaba wa kwmaishinoninsa da sauran mambobin majalisar zartarwa bisa namijin kokarinsu a wurin zaɓen na ranar Asabar.

Meyasa Shekarau ya ɓalle daga tsagin Ganduje?

Malam Shekaru, mai wakiltar mazaɓar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, ya jagoranci wata tawaga da ake kira G-7 domin kalubalantar Ganduje.

Tsagin shekarau ya ƙunshi Sanata mai wakiltar Kano ta arewa, Bara'u Jibrin, Mambobin majalisar wakilan tarayya huɗu, da sauran wasu jiga-jigan APC a Kano.

Sun aike da saƙon ƙorafi ga sakateriyar APC ta ƙasa, duba da irin gudummuwar da suka bayar wajen nasarar jam'iyyar a 2019, amma a ware su a harkokin jam'iyya na jihar.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

Rikicin dai ya ƙara ƙamari ne, bayan gangamin taron APC na jihar ya fitar da shugabanni biyu daga tsagin Ganduje da kuma na shekarau wato G-7.

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban PDP da wasu manyan shugabanni sun sauya sheƙa zuwa Jam'iyyar APC

A cewar waɗanda suka sauya shekan, ba bu wani dalili da zai sa su cigaba da zama cikin PDP, saboda shugaban ƙasa na bukatar goyon baya.

Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, kuma shugaban APC na ƙasa, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262