Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata
Zamfara - A ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, 2021, PDP ta reshen jihar Zamfara ta fito tana cewa akwai shiri a kasa na rusa mata hedikwata a Gusau.
Jam’iyyar PDP mai adawa ta zargi hukumar da ke kula da gine-gine a Zamfara watau the Zamfara State Urban and Regional Planning Board da wannan aikin.
Daily Trust tace sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Alhaji Farouk Ahmad Shattima ya shaida mata wannan da ya zanta da ‘yan jarida.
Kamar yadda Farouk Ahmad Shattima ya fadawa manema labarai, bayan sauya-shekar Bello Matawalle, an karbe ofishinsu, aka damka wa APC mai mulki.
Shattima yake cewa an sake wa hedikwatar jam’iyyar ta su fasali, an zana masa tambarin APC.
Wahalar da PDP ta ke sha a Gusau
“Daga nan sai muka zabi mu koma wani gini a kan babban titi, sai suka je cikin dare suka sake yi wa ofishin fenti, suka buga tambarin jam’iyyar APC.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A haka muka dawo kan wannan ofis, tun kafin mu biya Naira miliyan 10 na kudin haya, muka rubuta wa hukumar ZUREPB takarda, muka sanar da ita.”
“Mun nemi izini, amma ba a ba mu amsa har na tsawon wata guda. Muka yi wa ofishin fenti, sai yanzu jami’an ZUREPB suka zo, suna neman ruguza ginin.”
“Mun sanar da lauyoyinmu kan batun. Za mu san matakin da za mu dauka” - Farouk Shattima
Farouk Ahmad Shattima yace a dokar kasa, PDP tana da damar da za ta bude ofis a duk fadin kasar nan. Jami’in jam’iyyar yace ba su saba wata dokar ZUREPB ba.
Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP
Matasa za mu yi a 2023 - Fakai
An ji cewa matasan APC na shiyyar Arewa maso yamma sun sha alwashin goyon-bayan duk wani matashin da ya tsaya takara a 2023, ko da na shugaban kasa ne.
Hon. Abubakar Sadiq Fakai ya nuna idan zaben 2023 ya zo, sai inda karfinsu ya kare muddin matashi ya na neman wata kujera, domin su ne su ka fi kowa yawa.
Asali: Legit.ng