Ana rade-radin Atiku zai dauki mutumin Tambuwal a matsayin ‘dan takarar mataimaki

Ana rade-radin Atiku zai dauki mutumin Tambuwal a matsayin ‘dan takarar mataimaki

  • Hon. Emeka Ihedioha zai iya zama wanda zai taya Atiku Abubakar shiga takara a zabe mai zuwa
  • Akwai kishin-kishin cewa tsohon Gwamnan na jihar Imo shi ne wanda Atiku Abubakar zai dauka
  • Emeka Ihedioha ya rike mataimakin shugaban majalisar wakilai a 2011 a lokacin Aminu Tambuwal

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja – ‘Dan takarar PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar yana la’akari da Rt. Hon. Emeka Ihedioha a sahun abokan takararsa a 2023.

Rahoton da Legit.ng ta samu shi ne ana maganar Atiku Abubakar zai iya dauko tsohon mataimakin shugaban majalisa, Emeka Ihedioha.

Hon. Emeka Ihedioha ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayyar kasar nan a lokacin da Aminu Waziri Tambuwal ya rike majalisa.

Ana kyautata zaton Aminu Waziri Tambuwal ya kawowa ‘dan takarar shugaban kasar wannan shawara cewa ya tafi da 'dan shekara 57 a zaben 2023.

Sannan Ihedioha ya na cikin wadanda suka matsawa Gwamnan Sokoto ya hakura da neman tutar PDP na shugaban kasa, ya janyewa Atiku Abubakar.

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP sun shirya zaben Aminu Tambuwal a matsayin ‘dan takara domin yana tare da tsohon gwamnan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da Emeke Ihedioha Ihedioha New Media Centre
Asali: Facebook

Da Tambuwal ya janye takarar, sai magoya bayan na sa suka ba Atiku da ya yi nasara kuri’unsu.

Idan wannan labari ya zama gaskiya, tun bayan kammala zaben fitar da gwani, Aminu Tambuwal ya bijirowa Atiku da maganar ‘dan takarar mataimaki.

Wata majiya ta shaida cewa bangaren Gwamnan na Sokoto sun ba Atiku sunan Ihedioha. Da farko ana zargin ‘dan takarar bai gamsu da wannan zabin ba.

Haka zalika ana zargin tsohon ‘dan majalisar tarayyar ya yi watsi da wannan tayi a tashin farko.

Emeka Ihedioha shi ne wanda INEC ta ayyana a matsayin wanda ya ci zaben gwamnan Imo. Daga baya kotun koli ta tsige shi, ta daura Hope Uzodinma.

Kafin yanzu masu fashin bakin siyasa su na tunanin Ihedioha zai nemi ya gwabza da Hope Uzodinma a zaben gwamnan jihar Imo da za ayi a 2023.

Okowa ko Udom Emmanuel

A baya kuma kun ji labari cewa ana tunani ‘Dan takarar na PDP zai zakulo abokin takararsa ne daga yankin kudu maso kudancin kasar na Neja-Delta.

Daga cikin zabin akwai Gwamna Udom Emmanuel wanda ya yi takara da Atiku wajen samun tikiti, sai kuma Gwamnan Delta, Sanata Ifeanyi Okowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel