Ku taimaka mun da goyon baya na gaji Buhari a 2023, Gwamna ya roki Mambobin APC

Ku taimaka mun da goyon baya na gaji Buhari a 2023, Gwamna ya roki Mambobin APC

  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki shugabannin APC na jiharsa su fara nuna masa soyayya game da takara a 2023
  • Bello, ɗaya daga cikin waɗan da suka ayyana takarar kujerar shugaban ƙasa, yace ya kamata gida su fara nuna masa tsantsar goyon baya
  • Ya ce matukar mutane suka tasa abu a gaba da yakini, da izinin Allah za su ci nasarar wannan abun cikin sauki

Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, a ranar Alhamis, ya roki mambobin jam'iyyar APC na jiharsa su ba shi cikakken goyon baya ya samu nasarar zama shugaban ƙasa a 2023.

Vanguard ta ruwaito cewa Bello ya yi wannan rokon ne a wurin taron rantsar da mambobin majalisar zatarwan APC na jihar a hukumance a Sakatariya dake Lokoja.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Gwamna Yahaya Bello na Kogi
Ku taimaka mun da goyon baya na gaji Buhari a 2023, Gwamna ya roki Mambobin APC Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

A kalamansa na wurin taron, gwamna Bello ya ce:

"Babban aikin da muka sa a gaba shi ne ɗarewa kujerar shugaban ƙasa, ya zama wajibi mu ɗauke shi dagaske, mu sa yaƙini a zuciya domin zaɓen 2023 kara kusantowa yake."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na faɗi haka ne sabida duk abin da mutane suka sa a ransu kuma suna da yaƙini to za su samu nasara da yardar Allah."

Kada ku gaji da goyon bayan APC - Gwamna Bello

Bello, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, David Edward-Onoja, ya bukaci mambobin jam'iyya ka da su nuna gajiya wajen goyon bayan APC.

"Saboda duk kokarin taimaka wa jam'iyya da kuka yi, to ta wata hanyar kuna taimaka mun ne a matsayina na gwamnan ku."

Gwamnan ya kuma bukaci sabbin shugabannin APC na jihar su sadaukar da kansu wajen haɗa kan jam'iyya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Kara karanta wannan

Manyan jiga-jigan APC da Mambobi sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya

Ya kuma yaba wa shugabannin baki ɗaya sabbi da waɗan da suka sauka, bisa namijin kokarin da suka yi da juriya wajen tabbatar da nasarar APC a jihar Kogi.

Shin babu rikici a APC ta Kogi?

Tun da farko, sabon shugaban APC a jihar Kogi, Abubakar Bello, a madadin sabbin shugabanni, ya ce ba zasu gaji ba za su cigaba da bakin kokarin su wajen haɗa kan APC.

A wani labarin na daban kuma Daga karshe, Tsohon gwamna ya bayyana jam'iyyar da ya koma bayan ficewa daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, yace ya shiga jam'iyyar SDP kuma zai nemi takarar gwamna a zaɓen 18 ga watan Yuni.

Oni ya sanar da cewa jiga-jigan manyan jam'iyyun APC da PDP na goyon bayan takararsa ta gwamnan Ekiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262