Daga karshe, Tsohon gwamna ya bayyana jam'iyyar da ya koma bayan ficewa daga PDP
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, yace ya shiga jam'iyyar SDP kuma zai nemi takarar gwamna a zaɓen 18 ga watan Yuni
- Oni ya sanar da cewa jiga-jigan manyan jam'iyyun APC da PDP na goyon bayan takararsa ta gwamnan Ekiti
- Tsohon gwamnan ya fice daga jam'iyyar PDP ne bayan rashin nasarar samun tikitin takarar gwamna, wanda Bisi Kolawale ya lashe
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, ya bayyana cewa ya shiga jam'iyyar SDP domin ya nemi takarar gwamna a zaɓen dake tafe ranar 18 ga watan Yuni, 2022.
Mista Oni, ya sanar da haka ne yayin da ya bayyana a shirin gidan Radio FM da aka watsa a tashar Voice 89.9 FM, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Tsohon gwamnan ya ce akwai sauran cike-ciken takardu da za'a kammala ba da jimawa ba tare da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) domin tabbatar da takararsa a SDP.
Meyasa ya zaɓi shiga SDP da yin takara?
Oni ya bayyana cewa ya ɗauki matakin shiga takara karkashin SDP ne saboda kiran da mutanen jiha ke masa, suna rokon ya shiga kowace jam'iyya ce ya nemi takara domin ceto su daga Talauci, rashin tsaro da sauran su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa ya ce:
"Na zaɓi cika muradi na karkashin SDP saboda muna hangen goben al'umma ne ba yanzu ba. Jam'iyyar ta jima ana fafatawa da ita tsawon shekaru kuma ta samu nasara a kujeru da dama na ƙasar nan."
"Dan haka sananniyar jam'iyya ce shiyasa na zaɓi shiga SDP kuma na fafata a zaɓen 18 ga watan Yuni a jihar Ekiti. Matakan tsayar da ni takara a SDP sun yi nisa, nan ba da jima wa ba za'a kammala."
Akwai masu goyon bayana a APC da PDP - Segun Oni
Bayan sanar da shiga SDP, Oni ya yi ikirarin fusatattun ƴaƴan APC da PDP na goyon bayan takararsa na zama gwamna na gaba a Ekiti, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Duk da bai ambaci suna ba, tsohon gwamnan yace suna kokarin haɗa kai da yan takarar gwamna a APC da suka sha ƙasa, mambobin SWAGA, da wasu 'ya'yan PDP domin tabbatar da ya samu nasara a zaɓe mai zuwa.
A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan APC da Mambobi 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya
Yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaben 2023 dake tafe, Jam'iyyar PDP ta yi manyan kamu a jihar Bayelsa ranar Talata.
Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da kuma dubbannin mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa PDP a jihar.
Asali: Legit.ng