Manyan jiga-jigan APC da Mambobi 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya
- Yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaben 2023 dake tafe, Jam'iyyar PDP ta yi manyan kamu a jihar Bayelsa ranar Talata
- Wasu jiga-jigan APC da kuma dubbannin mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa PDP a jihar
- Tsohon kwamandan kwalejin sojoji dake Abuja na ɗaya daga cikin waɗan da suka jagoranci masu sauya shekar zuwa PDP
Delta - Tsohon Kwamandan kwalejin Sojoji dake Abuja, Rear Admiral Thomas Lokoson mai ritaya, da kuma mambobin APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Bayelsa.
Daily Trust ta rahoto cewa Mista Lokoson ya fito ne daga yankin ƙaramar hukumar Ijaw ta kudu, a jihar Bayelsa.
Ya ce ya ɗauki matakin dawowa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne saboda inganci da amincewa da yanayin yadda Gwamna Diri ke tafiyar da mulkin jihar cikin salo mai kyau.
Tsohom kwamandan na ɗaya daga cikin jiga-jigan APC da suka jagoranci mambobi sama da 5,000 zuwa jam'iyyar PDP a wurin wani taron zagaye a Yenagoa ranar Talata.
Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, shi ya jagoranci Diri da wasu gwamnonin PDP suka karɓi masu sauya sheƙan a wurin taron.
Rahotanni sun nuna cewa an shirya taron ne domin murnar cikar gwamna Diri na jihar Bayelsa shekara biyu a kan mulki.
Meyasa suka koma PDP?
Da yake zantawa da manema labarai bayan sauya shekar su, Lokoson ya ce ya shiga APC ne tun farko ba tare da niyya ba, kuma bai ga ta zama a cikin jam'iyyar ba.
Ya ce:
"A yau na ji ni garau, na ɗana dukka jam'iyyun nan biyu kuma na san kowace daga ciki, jam'iyyar PDP ce zaɓi na na ƙarshe, ba sauran tantama."
A cewarsa alamomin da gwamna ke nuna wa da yadda yake tafiyar da gwamnatinsa, sun tabbatar da cewa akwai jagoranci mai kyau a jam'iyyar.
A wani labarin kuma Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi gaskiyar abin da ya faru
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC, da jagororinta.
Atiku, wanda ya yi karin haske ta bakin kakakinsa, Paul Ibe, yace ya je ta'aziyyar mahaifiyar Mangal a Katsina, kuma ya haɗu da jagororin APC a can.
Asali: Legit.ng