Sanata ta fusata, gwamnoni da Sanatoci sun haɗa ta da Allah kada ta fice daga PDP

Sanata ta fusata, gwamnoni da Sanatoci sun haɗa ta da Allah kada ta fice daga PDP

  • Manyan jiga-jigan PDP sun fara kokarin hana Sanata Olujimi mai wakiltar kudu ta yammacin Ekiti daga shirin ficewa daga PDP
  • Sanatan ta fusata da jam'iyyar PDP ne tun bayan zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamnan jihar Ekiti da ya gudana a baya
  • Tsohuwar shugabar marasa rinjaye ta ce manyan mambobin PDP sun fara neman hana ta sauya sheƙa

Ekiti - Jagororin jam'iyyar PDP sun fara hana kansu bacci a kokarin hana sanata mai wakiltar Eikiti ta kudu, Biodun Olujimi, sauya sheka daga jam'iyyar, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Rahotanni sun bayyana cewa manyan jiga-jigan PDP na koƙarin hana sanatan barin jam'iyyar PDP a wannan lokacin.

Wasu gwamnoni da sanatoci sun fara tattaunawa domin duba hanyoyin daƙile shirin tsohuwar shugabar marasa rinjaye na komawa wata jam'iyya daban.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

Sanata Biodun Olujimi
Sanata ta fusata, gwamnoni da Sanatocin sun haɗa ta da Allah kada ta fice daga PDP Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Suwa suka fara kokarin hana ta sauya sheka?

Wata majiya ta ce tsohon gwamna, Ayodele Fayose, da kuma mataimakin shugaban PDP na kudu-yamma, Soji Adagunodo, sun tuntubi Olujimi domin ta sake tunani.

Haka nan a bangaren ta, wata majiya ta tabbatar da cewa Fayose da Adagunodo, sun tuntuɓi Olujimi, sun bukaci ta canza tunani game da ficewa daga PDP.

"Ana cigaba da ƙoƙarin hana sanata Olujimi da magoya bayan ta fita daga PDP. Jagororin mu daga ciki da wajen jihar Ekiti na matukar kokari na ganin sun dakatar da ita."

Sanata Olujimi ta tabbatar da lamarin

Da muka nemi jin ta bakinta a wayar salula, Sanata Olujimi, ta tabbatar da cewa wasu gwamnoni da sanatocin PDP sun matsa mata ta canza tunani.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kotu ta yi watsi da bukatar mataimakin gwamna Matawalle da jam'iyyar PDP

Sanatan ta ce:

"Har yanzun muna cigaba da tattauna wa, ba zan ɗauki mataki kan lamarin cikin gaggawa ba."

Kakakin tsohon gwamna Fayose, Lere Olayinka, ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya nemi Sanatan domin daƙile shirinta na sauya sheƙa.

A wani labarin na daban kuma Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi aihinin abin da ya faru

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC, da jagororinta.

Atiku, wanda ya yi karin haske ta bakin kakakinsa, Paul Ibe, yace ya je ta'aziyyar mahaifiyar Mangal a Katsina, kuma ya haɗu da jagororin APC a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel