PDP 2023: Gwamnan Arewa dake son gaje kujerar Buhari ya shiga Kebbi, ya samu gagarumin goyon baya
- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya kai ziyara jihar Kebbi game da kudirinsa na neman shugaban ƙasa a 2023
- Gwamnan ya gana da shugabannin PDP na jihar, kuma sun amince sun tabbatar masa da goyon bayan ya dare kujera lamba ɗaya
- Baki ɗaya shugabannin PDP reshen jihar tun daga matakin gunduma har jiha suka fito suka tarbi gwamnan
Kebbi - Jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta nuna goyon bayan ta ga takarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a zaɓen 2023.
Vanguard ta rahoto cewa Tambuwal ya kai ziyara Kebbi ne da safiyar Talata, yayin da yake cigaba da yawon neman shawari da goyon baya a faɗin kasar nan.
Gwamna ya je jihar tare da tawagarsa da suka haɗa da tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon mataimkain gwamna kuma tsohon ministan albarkatun ruwa, Muntari Shagari, da sauran su.
A jawabinsa yayin gana wa da baki ɗaya shugabannnin PDP na Kebbi, gwamnan yace ya kawo ziyara ne domin neman shawari kan kudirinsa na neman kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Ya kuma ƙara da cewa duba da yadda ya sha mamakin tarbar da ya samu daga shugabannin PDP da al'umma, ya ji kwarin guiwar cewa jam'iyya ta dawo kan turba a jahar.
Tambuwal ya jaddada cewa matukar kowa ya zo aka haɗa kai wuri ɗaya, to PDP zata kwace mulkin Kebbi da ma Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan ya ce:
"APC ta ba Najeriya kunya. Kungiyoyin duniya sun sanya wa Najeriya babbar ƙasar Talauci kuma lokaci ya yi da zamu canza zancen."
"PDP ta jagoranci Najeriya a baya kuma yanzu ga APC a kan madafun iko, kowa ya na kallon banbanci a fili. Alƙawarin da suka yi a yaƙin neman zaɓe sun gaza cikawa."
"Saboda haka lokaci ya yi da zamu canza canji domin gyara ƙasar mu. Ina rokon ku cigaba da haɗa kan ku kuma ku sadaukar da kan ku ga ƙasa."
Muna goyon bayanka a 2023 - Shugaban PDP
A nasa jawabin, shugaban PDP reshen jihar Kebbi, Usman Bello Suru, ya ce baki ɗaya jagorancin jam'iyya na Kebbi na goyon bayan takarar gwamna Tambuwal.
Ya nuna haka a aikace, inda ya bukaci wakilai, shugabannin PDP na matakin jiha, kananan hukumomi da gunduma su bayyana kansu don tabbatarwa.
A wani labarin na daban kuma Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekar Gwamna Matawalle zuwa jam'iyyar APC
Babbar Kotun tarayya dake Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ta yi fatali da ƙarar da aka shigar gabanta kan sauya shekar gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.
Alkalin Kotun, Mai Shari'a Aminu Aliyu, yace Kotu ba ta da hurumin shiga lamarin siyasa da ya shafi jam'iyyu, dan haka ba abin d azata iya yi.
Asali: Legit.ng