A karon farko, Mace yar shekara 38 ta bayyana kudurinta na zama shugaban kasa a 2023
- A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai a 1960
- Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a zaben 2023
- Khadijat ta kasance mai fafutukar yancin matasa da samar musu cigaba, kuma ta yi ƙaurin suna musamman a kafafen sada zumunta
Lagos - Wata mai fafutukar cigaban matasa yar kimanin shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta zama mace ta farko da ta bayyana sha'awar takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Litinin, Khadijat ta fito fili ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a kujera lamba daya ta Najeriya.
Matashiyar ta kasance mace ta farko mai kamar maza, da ta bayyana fatan ganin ta gaji shugabancin Najeriya a babban zaben dake tafe, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Wacece Khadijat Lamidi?
Rahoto ya nuna cewa Khadijat ɗiya ce ga babban lauya, Lateef Femi Okunnu (SAN), tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje na tarayya.
Haka nan kuma mahaifinta shine shugaban kungiyar Isale-Eko kuma dattijon ƙasa ne da ya dade yana bada gudummuwa.
Mahaifiyar Khadijat mai suna, Arinola Omololu, ta kasance babbar yar kasuwa a yankin Ago-Owu.
Yaushe ta bayyana cewa zata fafata a zaben shugaban kasa?
Da take jawabi a wurin taron manema labarai da ya gudana a Freedom Park dake jihar Legas, Khadijah Okunnu-Lamidi ta bayyana cewa zata tsaya takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.
A cewarta babban abin da ya kara mata kwarin guiwar neman takarar shugaban kasa ya samo asali ne daga muradinta na inganta Najeriya ta yi aiki ga jama'arta maban-banta.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Ribas yace ko ta wane hali sai jam'iyyar PDP ta dare mulkin Najeriya a babban zaben 2023
Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas, yace jam'iyyar PDP ba zata taba yarda da shan ƙasa ba a babban zaben 2023 saboda yan Najeriya sun dogara da ita a matsayin jam'iyyar da zata zo ta cece su.
Gwamnan yace yan Najeriya sun zama abin tausayi, waɗan da ba su da wata kyakkyawar makoma a hannun masu garkuwa da yan bindiga.
Asali: Legit.ng