Kano Ta Cika Makil, Manyan Najeriya Sun Dura Auren 'Ya'yan Kawu Sumaila

Kano Ta Cika Makil, Manyan Najeriya Sun Dura Auren 'Ya'yan Kawu Sumaila

  • An daura auren ‘ya’yan Sanata Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Sarina a Sumaila, Jihar Kano, tare da halartar manyan mutane daga fadin Najeriya
  • Manyan sanatoci da jiga-jigan siyasa sun samu halarta, ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, da mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin
  • Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan ‘yan siyasa sun halarci bikin, inda suka taya sababbin ma’auratan murna da fatan alheri

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A ranar Asabar an daura auren ‘ya’yan Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Yunusa Sarina a garin Sumaila na Jihar Kano.

Bikin daurin auren ya samu halartar manyan mutane, ciki har da jiga-jigan siyasa daga majalisar dattawa da gwamnatin tarayya, wadanda suka zo domin taya sabbin ma’aurata murna.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

Kawu Sumaila
An daura auren 'ya'yan Kawu Sumaila a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya jagoranci tawagar sanatoci da suka halarci bikin kamar yadda ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da daurin auren ne a Masallacin Juma’a na Sumaila karkashin jagorancin Farfaesa Salisu Shehu.

Jiga-jigan 'yan siyasa hun halarci bikin

Bikin auren ya kasance daya daga cikin manyan tarukan da suka hada kan jiga-jigan siyasa a Najeriya, inda manyan sanatoci suka hallara domin taya amare da angwaye murna.

Daga cikin sanatocin da suka halarci bikin akwai Sanata Muhammed Tahir Mungono, Sanata Abba Moro, Sanata Ahmed Lawan, Sanata Abdul Ningi, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Haka zalika akwai Sanata Victor Umeh, Sanata Danjuma Goje, Sanata Eze Kenneth, da Sanata Nasiru Sani Zangon Daura.

Auren
Sanata Goje da manyan baki a garin Sumaila. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Haka nan, wasu daga cikin sanatocin da suka samu halarta sun hada da Sanata Ekong Samson, Sanata Khalid Ibrahim, Sanata Khabib Mustapha, Sanata Sahabi Yau.

A daya bangaren akwai Sanata Abdulhamid Mallam Madori, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, da Sanata Shehu Buba.

Kara karanta wannan

Bayan saukar farashi, an kawo tallafin abinci na Dala miliyan 1 jihohin Arewa

Halartar irin wadannan mutane a bikin aure na nuni da yadda Sanata Kawu Sumaila ke da kusanci da manyan ‘yan siyasa a Najeriya, da kuma yadda ake mutunta shi a fagen siyasa.

Shugaban APC da manyan baki wajen bikin

Bikin auren bai tsaya ga sanatoci kawai ba, domin kuwa ya samu halartar jiga-jigan siyasa daga jam’iyyar APC da sauran bangarori na gwamnati.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, CFR, yana daga cikin manyan baki da suka halarci bikin, tare da sauran shugabanni na jam’iyyar APC daga sassa daban-daban.

Baya ga hakan, manyan ‘yan siyasa daga Kano da sauran jihohin Arewa sun halarta domin taya Sanata Kawu Sumaila da Alhaji Abdulmanaf Yunusa Sarina murna.

Addu’a ga amare da angwaye

A yayin daurin aure, an gudanar da addu’o’i na musamman domin rokon Allah Ya albarkaci zaman aurensu da kuma sanya musu farin ciki da fahimtar juna.

Kara karanta wannan

Yadda jiga jigan Najeriya suka tara Naira Biliyan 17 ga IBB a zama 1

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi addu’a Allah Ya ba ma’auratan zaman lafiya, hakuri, juriya, soyayya, da fahimta domin rayuwar aure mai albarka.

An daura auren 'yar Sanusi II

A wani rahoton, kun ji cewa manyan mutane sun cika a jihar Kano da aka daura auren a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi.

An daura auren Amina Muhammdu Sanusi II ne a jihar Kano kuma bikin ya samu halartar manyan baki a ciki da wajen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng