Kwankwaso, Barau da 'Yan Siyasar da Suka Aurar da 'Ya 'yansu a Shekarar 2024
Fitattun 'yan siyasa a fadin Najeriya sun aurar da 'ya'yansu a shekarar 2024 ciki har da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
An gudanar da bukukuwa da dama da ke alaka da manyan 'yan siyasa, 'yan kasuwa da malaman addini a shekarar 2024 mai shirin karewa.
Manyan 'yan siyasa da suka hada da Sanata Rabi'u Kwankwaso, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin sun aurar da 'ya'yansu.
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka aurar da 'ya'yansu a shekarar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Auren 'yar Sanata Muhammad Danjuma Goje
An daura auren Fauziyya Danjuma Goje da angonta, Aliyu Ahmed Abubakar a ranar Juma’a, 25 ga Oktoba, 2024, a Babban Masallacin Abuja.
Manyan jami’an gwamnati sun halarci daurin auren ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Obot Akpabio.
Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, gwamnoni da dama sun halarci auren.
Bola Tinubu ya ba da auren 'yan Goje
Hadimin Sanata Goje, Muhammad Adamu Yayari ya wallafa a Facebook cewa shugaba Bola Tinubu ne ya kasance waliyyin amarya.
Haka zalika tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Ibrahim Dankwambo, ya kasance wakilin ango a lokacin daurin auren.
2. Auren 'yar Sanata Rabi'u Kwankwaso
Legit ta rahoto cewa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba aka daura auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal.
An daura auren ne a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II kuma baki sun cika fadar daga ciki da wajen Najeriya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya kasance babban mai masaukin baki kuma shi ya kasance waliyyin amarya.
Manyan baki sun halarci auren 'yar Kwankwaso
Auren Dr Aisha Rabi'u Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal ya samu tururuwar manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun halarci daurin auren.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, tsofaffin gwamnoni, ministoci da Sanatoci sun shaida daurin auren.
Kwankwaso ya yi godiya bayan daurin aure
Bayan kammala daurin auren, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi godiya ga dukkan jama'ar da suka taso daga ciki da wajen Najeriya domin taya su murna.
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi addu'ar Allah ya mayar da kowa gida lafiya da kuma Allah ya ba amarya da ango zaman lafiya.
3.Auren 'ya'yan Sanata Barau Jibrin
An yidaurin auren ƴaƴan Sanata Barau da suka hada da Jibrin Barau I. Jibrin da Maryam Nasir Ado Bayero, da kuma Aisha Barau I. Jibrin da Abubakar Abdulmunaf Yunusa Sarina.
Sanata Barau ya wallafa a Facebook cewa an daura auren ne a ranar Juma'a, 13 ga Disamba a masallacin kasa da ke Abuja.
Limamin Masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ne ya jagoranci daurin auren bayan sallar Juma’a.
Bola Tinubu ya ba da auren 'yar Barau
Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya halarci daurin auren 'ya'yan Barau kuma shi ne wakili da waliyyin amarya da ango.
Sai dai shugaban kasar ya nada Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya wakilce shi wajen bayar wa da karbar auren.
Bakin da suka halarci auren 'ya'yan Barau
Gwamnoni, Sanatoci, 'yan Majalisar Wakilai, ƴan majalisar ECOWAS, da ministoci, har zuwa attajirai, sarakuna na gargajiya, da shugabannin addinai sun halarci bikin.
Shugabannin APC karkashin jagorancin DAbdullahi Umar Ganduje, wakilan shiyyar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawa ma sun halarci daurin auren.
Sanata Barau ya yi godiya ga mahalarta auren kuma ya yi addu'ar Allah ya ba ma'auratan zaman lafiya a rayuwar da za su yi.
4. Auren 'yar gwamna Umar Namadi
A ranar Juma'a, 20 ga Disamba, 2024 ne aka ɗaura auren 'yar gwamnan jihar Jigawa, Dr Salma Umar Namadi da Abba Sulaiman Musa Kadira.
Hadimin gwamna Umar Namadi, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook cewa an daura auren ne a babban masallacin Jumu'a na Dutse a kan sadaki N300,000.
Bakin da suka hallara daurin aure a Dutse
Ɗaurin auren ya samu halartar manyan baƙi daga ciki da wajen jihar Jigawa, wanda su ka haɗa da mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Katsina, Dr Dikko Umar Radda.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, gwamnan jihar Zamafara Dr. Dauda Lawal sun halarci bikin.
Tsofaffin gwamnonin jihar Jigawa, Dr Sule Lamido CON da Dr Ibrahim Saminu Turaki sun halarci daurin auren.
5. Auren dan Gwamna Sheriff Oborevwori
A ranar Asabar, 21 ga Disamba aka daura auren dan gwamnan jihar Delta Clinton Oborevwori a birnin Asaba.
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara na cikin manyan bakin da suka halarci bikin kamar yadda ya wallafa a Facebook.
Haka zalika gwamnonin Adamawa da Rivers na cikin manyan bakin da suka taya gwamna Sheriff Oborevwori murna wajen daurin auren.
Legit ta tattauna da malamin addini
Wani malamin addini a jihar Gombe, Ustaz Usman Muhammad ya ce akwai darasi da matasan Najeriya za su dauka a kan yadda manyan kasar suka aurar da 'ya'yansu.
Ustaz Usman ya ce ya kamata matasa su daina fada da juna a kan 'yan siyasa lura da yadda suke taruwa da auratayya a tsakaninsu.
Ya kara da cewa kamata ya yi matasa su mayar da hankali wajen gina rayuwa mai kyau kamar yadda 'yan siyasar suke yi wa 'ya'yansu.
An daura auren dan Kannywood
A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren mawakin Kannywood mai suna Abdul Respect a jihar Kano.
Legit ta wallafa cewa jaruman Kannywood da dama sun halarci daurin auren Abdul Respect da amaryarsa Hassana Abubakar Bulama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng