Barkwancin Tinubu Yayin Gabatar da kasafin 2025 Ya Jawo Ihu a Majalisa

Barkwancin Tinubu Yayin Gabatar da kasafin 2025 Ya Jawo Ihu a Majalisa

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kuskuren bayyana ‘yan majalisar tarayya na 10 a matsayin na 11 yayin gabatar da kasafin kudin 2025
  • Tinubu ya gyara kuskuren cikin barkwanci, inda ya lamarin ya sanya mahalarta taron gabatar da kasafin kudin fashewa da dariya
  • Kasafin kudin da aka gabatar ya kai ₦47.96 tiriliyan, wanda ya kunshi muhimman tsare-tsare na bunkasa tattalin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 a zauren majalisar dokoki ta tarayya.

A yayin gabatarwar, Tinubu ya yi kuskuren bayyana majalisa ta 10 a matsayin ta 11, lamarin da ya so kawo rudani kafin masa gyara.

Tinubu
Tinubu ya yi barkwanci yayin gabatar da kasafin kudin 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Rahoton Vanguard ya nuna cewa kasafin 2025 ya mayar da hankali kan habaka tattalin arziki da gyara sauran lamuran Najeriya.

Kara karanta wannan

Cikakken jawabin Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudin 2025 a Majalisar Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya gyara kuskure cikin barkwanci

Cikin kuskure shugaba Bola Tinubu ya ambaci 'yan majalisa ta 10 a matsayin 'yan majalisa ta 11 a yau Laraba.

Bayan da ‘yan majalisa suka ja hankalinsa kan kuskuren, Tinubu ya gyara cikin barkwanci, yana cewa:

“10? Na ce 11, hakan na nuna cewa duk an sake zabeku zuwa majalisa ta 11”

Wannan kalami nasa ya rage yanayin rashin annashuwa na zaman, ya kuma kawo dariya a zauren majalisar.

Bola Tinubu ya fara jawabinsa da cewa:

“A matsayin daya daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya daura a kaina, na gabatar da kasafin kudin 2025 a yau domin tabbatar da ci gaban Najeriya.”
Tinubu
Shugaba Tinubu yana jawabin gabatar da kasafin 2025 a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Muhimman abubuwan da kasafin ya kunsa

Leadership ta wallafa cewa kasafin ya kunshi tsare-tsare na gyaran kasa da bunkasa tattalin arziki, wadanda za a tattauna a zamanan majalisar masu zuwa.

Kara karanta wannan

Zargin karkatar da N111.8bn: Majalisar wakilai ta shirya binciken gwamnatin Tinubu

Ana sa ran cewa kasafin zai yi tasiri kan bangarori daban-daban na tattalin arzikin Najeriya, ciki har da harkokin tsaro, ilimi, da gyaran hanyoyi.

‘Yan majalisa za su tattauna kan yadda za a rarraba kudaden domin tabbatar da amfani da su ta hanyoyin da suka dace.

Tinubu zai biya bashin N15.81tn a 2025

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin 2025 an gano cewa biyan bashi zai lakume kaso mai tsoka.

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed zai kashe Naira tiriliyan 15.81 a kasafin kudin 2025 domin biyan bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng