Nyesom Wike: Ministan Tinubu Ya Gigita 'Yan Najeriya da Rigar Kusan Naira Miliyan 3
- 'Yan Najeriya sun yi wa Nyesom Wike, ministan FCT martani bayan ya saka rigar kusan Naira miliyan uku
- Ministan ya halarci ƙaddamar da tashar mota ta Mabushi dake Abuja ne da wannan shigar wadda ta ja hankali
- Jama'a sun caccaki shigar da ministan ya yi saboda halin matsin da 'yan Najeriya suke ciki a wannan lokacin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya haifar da cece-kuce a soshiyal midiya bayan da ya saka rigar fam 1,499 ta Versace.
Ya haɗa rigar da wani wando launin bula da kuma hula launin madara inda ya bayyana a wani taro cike da gayu.
An hango ministan ne a wurin ƙaddamar da tashar mota ta Mabushi a cikin Abuja, kamar yadda rahoton Premium Times ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun haɗa da Mariya Mahmoud, ƙaramar ministar babban birnin tarayya, da Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilan Najeriya.
Farashin rigar Wike ya kai N3m
Matsakaiciyar rigar kwat ta Versace riga ce da a bayyane take nuna aji da zamanancin wanda ya saka ta.
Binciken farashinta a yanar gizo ya bayyana cewa, rigar ta kai darajar £1,499 ko kusan Naira miliyan 2.9 a kasuwar canji.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya gigita jama'a da wannan shiga inda 'yan Najeriya suka dinga mayar masa da martani.
Martanin 'yan Najeriya kan rigar Wike
Akwai martani na 'yan Najeriya da suka caccaki ministan Tinubu sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu a ƙasar.
Mawaƙin Najeriya Omah Lay ya taɓa saka irin rigar a watan Satumban 2023 yayin da ya bayyana a Wonderland‘s Autumn/Fall 2023.
A wani bidiyo da aka wallafa a Instagram, an ga Wike cikin abokansa yana rawa bayan an saka waƙar Flavour ta 2023 mai suna Big Baller, duk sanye da wannan rigar.
Ga wasu daga cikin martanin da Legit.ng ta tattaro daga manhajar X:
@fauzybash ta ce:
"Da a ce kuɗi na siyan kwarjini..."
@amos_nandul ya ce:
"Ka na sanya rigar N3m amma duka-duka mafi ƙarancin albashin 35,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi ka kasa biya."
@farouk_Aliyuu ya ce:
"Wayyo kuɗinmu."
An kama bindigu da ƙwayoyi a Ribas
A wani labari, hukumar kwastam ta ƙasa ta kama bindigogi masu tarin yawa tare da ƙwayoyi a tashar jirgin ruwa na Onne a jihar Ribas.
Shugaban hukumar, Bashir Adeniyi, ya tabbatar da cewa an taho dasu ne takanas tun daga ƙasar Turkiyya, kuma an boye su a cikin kayan gwanjo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng