Bayan Shekaru 15 da Tarewa a Dubai, Budurwa ta Dawo Najeriya Neman Miji
- Wata mata ta taso takanas zuwa Najeriya don neman mashinshini bayan shekaru da tarewa a Daular larabawa na birnin Dubai
- Matar ta wallafa wani bidiyo wanda ke nuna dawowarta kasar yammacin Afirka, inda ta bayyana dawowarta hannu ba komai
- Kamar yadda ta ce, ta dauki tsawon lokaci tana biyan uwar dakinta na tsawon shekarun da ta zauna a Dubai sannan ta dawo cikin koshin lafiya
Bayan kwashe shekaru 15 tana rayuwa a Dubai tare da biyan uwar dakinta kudi, wata budurwa ta dawo Najeriya.
Budurwar a TikTok ta sanar da dawowarta Najeriya ta hanyar yin wani bidiyo dake nuna lokacin da ta isa filin jirgin sama.

Source: UGC
Yayin bayyana yadda ta dawo hannu rabbana, budurwar ta ce ta dawo cikin koshin lafiya. Wacce ta dawon daga UAE ta bayyana yadda take neman miji nagari ido rufe a Najeriya.

Kara karanta wannan
Bidiyon Yadda Ta Kwashe Tsakanin Soja da Wata Budurwa Bayan Ta Zage Ta Gudu, Ya Kamo Ta
Bidiyonta yayi yawo a dandalin sada zumuntar tare da jawo cece-kuce yayin da mutane da dama suka mata fatan alheri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga bidiyon a kasa:
Martanin 'yan soshiyal midiya
amejumatimeyin ta ce:
"Yar uwata babu miji a Najeriya, ki yi kokarin komawa Dubai ko ki na so ki yi biyu babu ne."
Lord lethal ya ce:
"Wasa ake gara ma ki koma ko kuma ki yi shekaru 30 ba miji sai dai gantali."
user762725512514 ya ce:
"Kada ki yanke tsammani... muna da mazan kwarai a Najeriya kuma za ki hadu da shi."
Frank peter ya ce:
"Kin je kin gama yawon ta zubar ne yanzu za ki nemi mijin da zai aje ki a gida? wasa kike."
simon_Ezoba ya ce:
"Ki yi imani da za ki samu miji nagari saboda babu wanda ya san gobe."
Micoolj ya ce:
"Shekaru 15!!! Uwar dakin ki na da wayau fa. Ina miki fatan alheri a neman abokin rayuwar da ki ke."

Kara karanta wannan
Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya
Brooklyn ya ce:
"Tambayata ita ce me yasa za ki tsaya a wani wuri tsawon lokacin nan amma ba ki da wani abu da za ki nuna."
Fasnjoji sun ragargaza bas bayan mai mota ya tsere da kudinsu
A wani labari na daban, wasu fasinjoji sun bada mamaki bayan sun babballe motar wani direba a Legas.
An gano cewa yayi sama da fadi da makuden kudadensu da suka tara masa matsayin na mota.
Asali: Legit.ng