Bidiyo: Nasir El Rufai Ya Isa Kotun Kaduna, Ya Yi Magana kan Babban Taron ADC

Bidiyo: Nasir El Rufai Ya Isa Kotun Kaduna, Ya Yi Magana kan Babban Taron ADC

  • Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa babbar kotun jihar Kaduna yau Litinin domin ci gaba da shari’ar da hukumar ICPC ke yi da shi
  • Wani bidiyo ya nuna El-Rufai cikin shigar fafaren kaya da babbar riga yayin da magoya baya da lauyoyi suka kewaye shi a harabar kotun
  • A cikin bidiyon, an ji Nasir El-Rufai ya yi magana game da babban taron da jam’iyyar ADC za ta gudanar a ranar Talata, 14 ga Afrilu, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna – Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a yau Litinin, 13 ga Afrilu, 2026.

Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan (ICPC) ne suka isa kotun tare da tsohon gwamnan, don ci gaba da shari'ar da ake yi.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya nemi babbar Alkali Najeriya ta sauya mai kula da shari'arsa, ya bayyana dalili

El-Rufai ya isa kotun Kaduna inda ake ci gaba da shari'arsa da ICPC
Malam Nasir El-Rufai a lokacin da ya isa harabar babbar kotun Kaduna tare da jami'an ICPC. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

El-Rufai ya tabo batun taron ADC a kotu

Wani faifan bidiyo da Daily Trust ta wallafa a shafinta na X, ya nuna tsohon gwamnan sanye da babbar riga, yana ratsa cikin taron jama’a da suka haɗa da magoya bayansa, lauyoyi, da kuma masu sha’awar ganin yadda shari’ar za ta kasance.

Abin da ya fi ɗaukar hankalin manazarta siyasa shi ne wata tattaunawa da aka ji El-Rufai yana yi da ɗaya daga cikin na-kusa da shi jim kaɗan kafin ya shiga cikin babban zauren kotun.

A cikin tattaunawar, an ji tsohon gwamnan yana tambaya game da babban taron ƙasa na jam’iyyar adawa ta ADC.

"Gobe ne taronmu, ko?" El-Rufai ya tambaya.

Abokin tafiyar tasa ya amsa da cewa, "Eh gobe ne, Insha Allah."

Wannan magana ta tabbatar da cewa El-Rufai ya damu kwarai kan harkokin siyasar kasar da na jam’iyyar ADC duk da ƙalubalen shari’a da yake fuskanta.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

Kalli bidiyon a kasa:

ICPC ta yi sauye sauye a shari'ar El-Rufai

Jim kadan bayan kammala zaman kotun, lauyan El-Rufai, Ubong Esop Akpan, ya bayyana cewa an dage zaman zuwa ranar Talata, 14 ga Afrilu, 2025 domin sauraron bukatar beli.

Malam Nasir El-Rufai ya tabo batun taron jam'iyyar ADC yayin da ya isa harabar kotun Kaduna.
Malam Nasir El-Rufai ya na duba wata takarda jim kadan da isarsa kotun jihar Kaduna. Hoto: Kama Ibrahim Ahmadu
Source: Facebook

A wani bidiyo da Malam Iramrana U. Wakili ya wallafa a shafinsa na X, an ji Ubong Akpan ya na cewa:

"Kotu ta saurara kuma ta karbi takardar bukatar bada beli, kotu ta karbi dukkan koke koken wanda ake kara. Amma bangaren masu kara sun yi sauye sauye a shari'ar.
"Sun cire mutum daya daga shari'ar, yanzu ya rage iya Malam El-Rufai ne kawai ake shari'ar da shi. Abin da ya faru kenan. An dage zaman zuwa gobe (Talata) don yanke hukunci kan bukatar belin da aka gabatar.:

Kalli bidiyon a nan kasa:

El-Rufai na ya roki a sauya alkali

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya rubuta takarda ga shugabar alkalan Najeriya inda ya nuna rashin gamsuwa da yadda ake shari'arsa.

Kara karanta wannan

Siyasa ta ɗau zafi: Kwankwaso ya sa DSS ta tsare wasu manyan hadiman gwamnan Kano

Gwamnatin Najeriya na shari'a da Nasir El-Rufa'i bisa zarge-zargen almundahana, karkatar da kudin jama'a da halasta kudin haram a wata kotun Kaduna.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana da babban korafi a kan alkalin da ke sauraron shari'ar tare da rokon Kudirat Kekere-Ekun ta kawo masa agaji ta hanyar sauya alkalin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com