An Rufe Masallatai 20, Mutane Sun Tsere daga Garuruwa 39 a Jihar Kaduna
- Mutane sun tattara kayansu, sun tsere daga ƙauyuka 39 a jihar Kaduna sakamakon hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane
- Fiye da mutane 1,000 aka sace daga ƙarshen 2025 zuwa yanzu, inda al'ummar yankin suka biya kusan Naira miliyan 300 na kuɗin fansa
- Tashin hankalin ya janyo rufe masallatai sama da 20 da majami'u sama da 65, yayin da mutane da dama suka tsere zuwa kwambta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna – Mazauna ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna sun yi kira na gaggawa ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki bayan wasu hare haren ƴan bindiga da ya tilasta wa mutanen ƙauyuka 39 barin gidajensu.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a madadin al'ummar da abin ya shafa, Rev. Musa Hassan Shadari ya bayyana cewa hare-hare sun tsananta tun ƙarshen shekarar 2025.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun tashi ƙauyuka 39 a Kaduna
A cewar Rev. Musa Shadari, ƴan bindiga sun ci gaba da addabar yankin a wannan shekarar ta 2026, inda suka rika kashe mutane da sace wasu, in ji rahoton Leadership.
Daga cikin ƙauyuka 39 da ya ce mutane sun tsere, Shadari ya lissafa guda 10 da ƴan bindiga suka mamaye yanzu:
- Unguwa Kunkun
- Unguwa Dutsen Yelwa
- Unguwa Samaila
- Unguwa Bulus
- Unguwa Pastor
- Unguwa Haske
- Unguwa Luku
- Unguwa Randa
- Unguwa Nasarawa
- Unguwa Doka
Mutane sun biya N300m na kuɗin fansa
Ya ƙara da cewa sama da mutane 50 ne suka rasa rayukansu tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban shekarar da ta gabata, kuma har yanzu mutane 17 suna hannun masu garkuwa da su.
Inji Rev. Shadari, wannan rashin tsaro ya raunana rayuwar addini a yankin, inda aka tilasta rufe masallatai sama da 20 da kuma majami'u sama da 65.

Kara karanta wannan
Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200
Wani abin ban tsoro da ya fito fili shi ne adadin kuɗaɗen da al'ummar yankin suka biya a matsayin kuɗin fansa. Shadari ya ce:
"Fiye da mutane 1,000 aka yi garkuwa da su, kuma har yanzu akwai mutane 17 a hannunsu. Mun biya kimanin Naira miliyan 300 a matsayin kudin fansa."
Haka kuma, wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Ho-re, ya ba da labarin yadda ya biya Naira miliyan 3.4 domin fansar ƴaƴansa uku da aka sace.

Source: Getty Images
Kiran al'ummar Kauru ga gwamnati
Mazauna yankin sun bayyana rashin jin daɗinsu kan yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu, in ji rahoton Trust Radio.
Sun bayyana cewa sojoji da ƴan sanda suna zuwa ne kawai idan hari ya riga ya faru, amma ba sa zama na dindindin domin kare ƙauyukan.
Sun nemi Gwamnatin Jihar Kaduna da ta jibge jami'an tsaro na dindindin a ƙauyukan domin ba su damar komawa gidajensu da ci gaba da harkokin noma.
'Yan bindiga sun tashi mutanen garuruwa 5
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai farmaki kauyuka biyar da ke yankin karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna, sun kori mutane daga gidajensu.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan majalisa ya ƙare kansa kan zargin fitar da bayan sirrin Najeriya ga ƙasashen waje
Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun ƙona kayayyakin mutane, sun kuma yi garkuwa da wasu matasa a kudancin jihar.
Shugaban al'umma a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ƴan bindigar sun shiga kauyukan ɗauke mugayen makamai, suka buɗe wuta.
Asali: Legit.ng
