"Ba Tabbas": Malamin Addini Ya Yi Hasashe kan Tazarcen Tinubu a 2027

"Ba Tabbas": Malamin Addini Ya Yi Hasashe kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Primate Ayodele ya yi gargadi kan shugaban kasar cewa akwai na kusa da shi wadanda ba sa gaya masa gaskiya
  • Malamin addinin ya bayyana cewa akwai wadanda ba sa sanar da shi gaskiyar abin da ke faruwa kuma hakan zai iya yi masa illa a shekarar badi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Primate Ayodele ya gargadi Tinubu da kada ya saki jiki game da burinsa na tazarce a wa’adi na biyu, domin har yanzu nasarar tasa ba ta tabbata ba.

Ayodele ya yi magana kan tazarcen Tinubu
Primate Elijah Ayodele na jawabi a wajen harkokin coci Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mataimakinsa kan yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Tinubu ya fadi abin da zai biyo bayan kisan janar a Borno

Me Ayodele ya ce kan tazarcen Tinubu?

Primate Ayodele ya bayyana cewa har yanzu wa’adi na biyu na Tinubu bai da tabbas, kuma na kusa da shi sun rufe masa idanu ta hanyar sihiri domin hana shi ganin ƙalubalen da ke gabansa.

Malamin addinin ya lura cewa batun rashin tsaro da tattalin arziƙi suna buƙatar dauki daga Ubangiji, amma idan Tinubu ya bar maƙaryata suka ci gaba da yaudararsa, sai bayan zaɓe ne idanunsa za su buɗe, wanda hakan na iya zama ya makara.

“Wa’adi na biyu na Tinubu yana tangal-tangal. Fannin tsaro yana buƙatar dauki daga Ubangiji, tattalin arziƙi ya shiga wani hali, sannan Tinubu yana kewaye da maƙaryata."
"Waɗancan mutanen da ke zuwa gare ka, suna rera maka waƙoƙin yabo, su ne makiyanka, kuma an rufe maka idanu ta hanyar sihiri."
“Ya kamata Tinubu ya samu wa’adi na biyu ba tare da wani cikas ba, amma an rufe masa idanu; sai bayan zaɓe ne idanunsa za su buɗe."

Kara karanta wannan

Ba labarin Kwankwaso, Atiku da Tinubu: Malami ya yi hasashen mai nasara a 2027

"Yawancin mutanen da ke shigowa jam’iyyarka sun zo ne don yi maka ba’a da kuma yi maka ƙarya cewa komai yana tafiya daidai."
"Masu tunani mara kyau da mayaudara sun matso kusa da kai, kuma za su yi maka ƙarya har sai ka tsinci kanka a cikin mawuyacin hali.”

- Primate Elijah Ayodele

Primate Ayodele ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu
Primate Elijah Ayodele na jawabi a coci Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Facebook

Yankunan da za su ba Tinubu matsala

Haka zalika, malamin ya bayyana cewa yankunan Kudu maso Gabas da Arewa za su zama babban ƙalubale ga shugaban ƙasar, kuma ba shi da tabbas ko akwai wata mafita gare shi, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

“Za ka fuskanci manyan matsaloli a Arewa da Kudu maso Gabas, waɗannan shiyyoyin ba su tabbata a gare ka ba tukuna, kuma ban sani ba ko akwai wata mafita."

- Primate Elijah Ayodele

Malamin addinin ya ba 'yan Najeriya shawara

Bugu da ƙari, Primate Ayodele ya buƙaci ’yan Najeriya da su koma ga Allah domin samun nasarar zaɓen 2027.

“Najeriya tana buƙatar dauki daga Ubangiji domin mu samu nasarar zaɓe. Najeriya tana buƙatar mutum irin Tinubu, amma sun gaji da shi saboda mugayen mutanen da ke kewaye da shi."

Kara karanta wannan

Kujerar mataimakin Abba Kabir na neman jawo rigima, an roki Tinubu kan Sule Garo

"Yana da kyakkyawar manufa ga Najeriya, amma sun rufe masa gani; ba ya iya hango abin da ke nesa."

- Primate Elijah Ayodele

Gwamna Abba ya yabi Tinubu

A wani labairn kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

Abba Kabir ya bayyana cewa Bola Tinubu shugaba ne mai ƙoƙari wanda ke samar da ribar dimokuraɗiyya a faɗin ƙasa ga jama’a.

Gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa Tinubu ya samu ci gaba wajen ƙarfafa tattalin arziki da bunƙasa manyan ayyukan more rayuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng