Gwamnatin Katsina Ta Shirya Gudanar da Auren Gata, Dubunnan Matasa Za Su Samu Mata

Gwamnatin Katsina Ta Shirya Gudanar da Auren Gata, Dubunnan Matasa Za Su Samu Mata

  • Gwamnatin jihar Katsina tare da hadin gwiwar wata kungiyar sa-kai sun shirya gudanar da auren gata ga mutane da dama
  • An shirya gudanar da auren gatan ne ga maza da mata domin rage aikata ayyukan alfasha da tallafawa mutanen da ba su da halin yin aure
  • A shirye-shiryen gudanar da auren gatan, an shirya taron karawa juna sani da horo ga masu shirin zama ma'auratan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta kammala dukkan shirye-shirye na gudanar da rukunin farko na auren gata.

Gwamnatin ta shirya auren gatan ne ga masu shirin zama ma'aurata 1,000 da aka zaɓo daga ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Gwamnatin Katsina ta shirya auren gata ga matasa
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce gwamnatin tare da haɗin gwiwar wata ƙungiyar sa-kai (NGO), Al-Usra Marital Support Foundation, sun shirya taron ƙarawa juna sani da horo na musamman ga masu shirin ma’aurata 1,000 da za su yi auren.

Kara karanta wannan

Bayan an kama su da ta'addanci, kotu ta sanar da ƴan Boko Haram 18 makomarsu

Ana shirin auren gata a Katsina

Shugabar ƙungiyar, Dr. Murjanatu Ibrahim-Duwan, ta bayyana cewa horon wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga watan Afirilun 2026, na nufin ƙarfafa martabar iyali da kuma rage yawan mace-macen aure (saki) a cikin al’umma.

Ta ƙara da cewa shirin zai ba wa masu shirin zama ma’auratan (mutane 2,000 kenan) ilimi da dabarun da ake buƙata don gina zaman lafiya da nasara a gidan aure.

Dr. Murjanatu ta ce ma’aikatar harkokin mata ta jihar ta riga ta tantance masu shirin zama ma’auratan tun da fari domin tabbatar da cewa kowannensu ya shirya kuma ya cancanci yin auren.

Wannan horo, wanda aka gudanar a shiyyoyin Katsina, Daura, da Funtua, wani ɓangare ne na shirye-shiryen ‘Auren Gata’, wanda gwamnatin jiha ta tsara gudanarwa a ranar 25 ga Afrilun 2026.

Amfanin shirin auren gata a Katsina

Tun da fari, Kwamandan Hisbah na jihar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), ya ce wannan shiri, wanda shi ne irinsa na farko a jihar, zai taimaka wajen rage ayyukan alfasha, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran/Isra'ila: Yawan asarar da Amurka ta yi yayin yaki a Gabas ta Tsakiya

Ya ƙara da cewa gwamnatin jiha za ta samar wa ma’auratan dukkan kayayyakin da ake buƙata don zaman aure, sannan za a ba wa ango jari don fara sana’a.

Abu Ammar ya lura cewa mata da yawa da suka haɗa da zawarawa, marayu, da sauran mutane marasa ƙarfi sun kasa yin aure duk da sha’awarsu saboda ƙalubalen tattalin arziki.

Ya ce bayan auren, hukumar za ta ci gaba da bin diddigin ma’auratan don tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnatin Katsina za ta gudanar da auren gata
Gwamna Dikko Umaru Radda a taron majalisar zartarwa ta Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

An yi musu gwaje-gwajen lafiya

Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Katsina, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta tabbatar da cewa dukkan masu shirin zama ma’aurata 1,000 sun yi gwaje-gwajen lafiya domin tabbatar da lafiyarsu da kuma dacewarsu da juna.

Kwamishinaiyar, wadda jami’ar yaɗa labarai ta ma’aikatar, Aminatu Sada Mashi ta wakilta, ta ce za a gudanar da wannan babban biki ne a ranar 25 ga Afrilu, 2026.

Sai dai har yanzu ba a bayyana adadin kuɗin da gwamnati ta ware don gudanar da wannan biki ba.

Kwamishina ya yi murabus a gwamnatin Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishina a jihar Katsina, Hamza Suleiman, ya yi murabus daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka kan ɗan Amurka da ke 'tunzura Kiristoci' a Jos

Kwamishinan muhalli, Hamza Suleiman, da mataimaki na musamman ga Gwamna Radda kan harkar miyagun kwayoyi da safarar mutane, Shehu Daura.

Bincike ya nuna cewa mutanen biyun suna shirin tsayawa takarar neman kujerar sanata ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng