Wasu Sun Rasa Abinci; Gwamna Inuwa Ya Rushe Majalisar Zartarwa

Wasu Sun Rasa Abinci; Gwamna Inuwa Ya Rushe Majalisar Zartarwa

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya raba mutanen da ke gwamnatinsa daga mukamansu bayan rushe majalisar zartarwa
  • Muhammad Inuwa ya sanar da rushe majalisar zartarwar ne a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026 yayin wani taro da aka gudanar
  • Matakin gwamnan dai na zuwa ne yayin da aka fara shirya buga kugen siyasa domin tunkarar babban zaben shekarar 2027 da ake fuskanta

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar zartarwa ta jihar.

Rushe majalisar zartarwar da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi, ya nuna wani gagarumin sauyi a yanayin siyasar jihar.

Inuwa Yahaya ya rushe majalisar zartarwa
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa an bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwa na jihar Gombe karo na 53, a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan ya yi murabus, Majalisa ta canza shawara kan mataimakin gwamnan jihar Kano

Gwamna Inuwa ya rushe majalisar zartarwa

Duk da cewa gwamnan bai bayyana dalilan rushe majalisar nan take ba, ana kyautata zaton matakin yana da alaƙa da wasu buƙatun siyasa da ke tasowa a tsakanin mambobin majalisar tasa.

Wannan matakin yana iya zama wani ɓangare na sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓubbuka masu zuwa a jihar.

Ana sa ran Gwamna Inuwa Yahaya zai sake kafa wata sabuwar majalisa a kwanaki masu zuwa domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati da kuma dorewar shirye-shiryen da ake kai.

Ana sa ran samun ƙarin bayani kan wannan matakin da gwamnan ya dauka.

An fitar da sanarwa

Hakazalika, Shugaban sashen na yaɗa labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya sanar da rushe majalisar zartarwar a cikin wata takaitacciyar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.

“Labari da dumi-duminsa.. Gwamna Inuwa Yahaya ya rushe majalisar zartarwa ta Gombe. “Ƙarin bayani na tafe.”

- Ismaila Uba Misilli

Kara karanta wannan

"Ba Kwankwaso ba"; An sanar da Gwamna Abba wanda zai sa ya lashe Kano a 2027

Gwamna Inuwa ya sallami masu mukamai a gwamnati
Gwamna Inuwa Yahaya da mukarrabansa a taron majalisar zartarwar jihar Gombe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Ba a bayyana dalili ba

Bayanai game da dalilan rushe majalisar ba su fito fili ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sai dai ana ran matakin zai shafi dukkan kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa na jihar dake kan mulki.

Ba a bayar da wani dalili na hukuma ba game da wannan shawara, amma masu sharhi na cewa irin waɗannan matakai galibi suna zama ɓangare na garambawul ga gwamnati ko kuma dabarun siyasa gabanin babban zaɓen 2027.

Karanta wasu labaran kan Gombe

Gwamna Inuwa ya ba Daurawa gida

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ba malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, gidan zama.

Kara karanta wannan

APC ta karbe ikon majalisa gaba daya da mamban PDP tilo ya koma jam'iyyar

Gwamna Inuwa Yahaya ya ba Sheikh Aminu Daurawa gida a Gombe ne bayan shafe sama da shekara 20 yana zuwa jihar tafsirin Ramadan duk shekara.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa 'yan kwanaki kafin shigar watan Ramadan shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya kira shi a waya cewa ya ba shi gida a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng