Akwai Kura: Shugaban INEC Ya Hango Babbar Barazana kan Zaben 2027

Akwai Kura: Shugaban INEC Ya Hango Babbar Barazana kan Zaben 2027

  • A Najeriya kallo ya fa komawa kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara nan da wasu watanni masu zuwa
  • Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce akwai abin da yake barazana ga zaben 2027
  • Farfesa Amupitan ya bayyana cewa akwai rawar da kafafen yada labarai za su taka wajen ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi gargadi kan zaben 2027.

Farfesa Amupitan ya yi gargaɗin cewa yaɗa bayanan ƙarya da kafafen yaƙada labarai ke ƙarfafawa na iya zama babban haɗari ga babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027.

Shugaban INEC ya yi magana kan zaben 2027
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a babban taron ƙungiyar gidajen yaɗa labarai ta Najeriya (BON) karo na 81 a Abuja ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Me shugaban INEC ya ce kan zabe?

Amupitan ya ce a halin yanzu ana yanke makomar sakamakon zaɓe ne a "wuraren yaɗa labarai," wanda hakan ya sa rawar da gidajen rediyo da talabijin ke takawa ta kasance mai matuƙar muhimmanci ga mutuncin dimokuraɗiyya.

Shugaban na INEC ya bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin "tubalin farko na dimokuraɗiyyarmu."

Hakazalika kuma ya yi gargaɗin cewa bayanan ƙarya, kalaman ƙiyayya, da rashin ba wa kowa damar amfani da kafafen yaɗa labarai daidai-wa-daida na iya gurgunta muradin masu zaɓe, rahoton jaridar Daily Trust ya nuna hakan.

“A babban zaɓen 2027, makami mafi haɗari ba zai kasance bindigar ɗan daba mai satar akwati ba, face ƙaryar mai amfani da wayar salula wadda gidan yaɗa labarai mara kishin gaskiya ya yaɗa ta."

- Farfesa Joash Amupitan

Amupitan ya yi magana kan dokar zabe

Ya bayyana wasu ɓangarori na dokar zaɓe ta 2026 da nufin magance waɗannan kasada, ciki har da wajabta ba wa jam’iyyun siyasa damar bayyana a kafafan yaɗa labarai daidai-wa-daida da kuma tsauraran hukunci ga masu katsalandan.

Kara karanta wannan

"Ba Kwankwaso ba"; An sanar da Gwamna Abba wanda zai sa ya lashe Kano a 2027

“Dokar ta wajabta adalci da daidaito. Dole ne ku samar da fili mai faɗi ga kowa."

- Farfesa Joash Amupitan

Ya ce dokar ta kuma mayar da kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a a matsayin laifi, inda take buƙatar masu yaƙin neman zaɓe su guji "amfani da kalaman cin mutunci da ka iya taɓa ra'ayin addini, ƙabila, ko na yanki".

Shugaban INEC ya yi maganganu kan zaben 2027
Farfesa Joash Amupitan a wajen taron INEC Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Akwai kalubale kan zabe

Shugaban na INEC ya ce duk da waɗannan tanade-tanade, akwai ƙalubale da suka rage, ciki har da raunin tabbatar da doka, sayar da lokacin yaɗa labarai ga masu kuɗi, da kuma mamaye kafafen yaƙada labarai da masu mulki ke yi.

Ya lura cewa “yan siyasa masu ɗumbin dukiya su ne suka mamaye kafafen yaɗa labarai,” lamarin da ke gurgunta ƙa’idar ba wa kowa dama daidai-wa-daida.

ADC ta yi zargi kan INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi zarge-zarge kan hukumar zabe ta INEC.

ADC ta zargi hukumar INEC da kitsa abin da ta kira tarko da gangan da nufin hana jam’iyyar gabatar da ’yan takara a babban zaɓen 2027.

Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar zaɓen da ɗaukar matsayi mai cin karo da juna ta hanyar dakatar da hulɗa da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng