NDLEA ta Kama Fasto da Matarsa Bisa Zargin Safarar Kayan Maye
- Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta cafke fasto da matarsa dauke da kayan maye
- An gano sun miyagun kayan mayen ne a cikin mota kafin daga bisani jam’an hukumar su yi ram da su tare da kwato kayan
- Jami’ai sun kama wasu da dama a farmakin yaki da fataucin kwayoyi a kasar nan, kamar dai yadda aka saba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jami’an Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wani fasto da matarsa a Legas bayan gano kilo 11 na tabar wiwi da aka boye a cikin sirrin sassan motarsu.
Wadanda aka kama sun hada da Fasto Afolabi Hodonu mai shekara 45, wanda ake zargin shi ne ke kula da cocin Celestial Church of Christ da ke Agonvi Sea Beach a yankin Sakpo na iyakar Seme a Badagry, da kuma matarsa, Misis Success Hodonu mai shekara 35.

Source: UGC
An kama su ne ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a wurin binciken ababen hawa na Gbaji, kamar yadda Legit Hausa ta gano a shafin hukumar NDLEA.
Bayanai daga hukumar NDLEA
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce binciken da aka yi wa motarsu kirar Honda Pilot ya kai ga gano kayan mayen da aka boye a cikin sassan mota.
Ya ce:
“An kama Fasto Afolabi Hodonu da matarsa Success Hodonu a ranar 2 ga watan Afrilu a wurin binciken Gbaji. Binciken motarsu ya kai ga gano kilo 11 na tabar wiwi da aka boye a sassan motar.”
Babafemi ya kara da cewa kamen ya biyo bayan wani lamari da ya faru a baya a wannan wurin, inda aka kama wani da ya yi karyar kasancewa jami’in tsaro mai suna Sunday Samuel mai shekara 35, dauke da kilo 24.5 na wiwi daga iyakar Seme zuwa Legas.
Yadda aka kai ga kame fasto da matarsa
Ya ce binciken da aka yi kan wannan kame ne ya kai ga gano faston da matarsa da ke harkallar kayan maye.
Ya kara da cewa wannan na daga cikin jerin ayyukan da hukumar ta gudanar a makon da ya gabata a fadin Najeriya.
A wani aiki makamancin haka, jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja sun kama kilo 3.10 na hodar iblis da aka boye a cikin gwangwanin man kwakwa da aka nufa kaiwa kasar Birtaniya.
An kuma kama wasu mutum biyu, Idris Olayiwola Amoo da Akinlami Akinsoji Adedoyin, yayin da bincike ya kai ga cafke wanda ake zargin ya tura kayan, Ezemuwo Joel, da kuma jagoran harkallar, King Arinze mai shekara 52, a Isolo da ke Legas.
An kuma gano kayayyaki da suka hada da gwangwani 886 da aka shirya domin boye kwayoyi da kuma kayan aikin nade su a wurin ajiyar kayan.
An kama mai kaiwa 'yan ta'adda kayan maye
Haka kuma, Babafemi ya ce jami’an sun kama wata mata mai shekara 28 mai suna Aisha Adamu a jihar Borno, wacce ake zargi da samar da miyagun kwayoyi ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki tsakanin Arewa maso Gabas da kasar Chadi.
An kama ta ne a kan hanyar Gamboru Ngala dauke da kilo 4.3 na wani nau’in wiwi mai karfi da ake kira Colorado.
Hukumar ta kuma sanar da Karin ayyukan da ta yi da suka kai ga kame gungu daban-daban na masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
Asali: Legit.ng


