Ke Duniya: Matashi Ya Kone Mahaifinsa Har Lahira a Jihar Jigawa
- Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi da ake zargi da kona mahaifinsa a jihar Jigawa, Arewacin Najeriya
- Lamarin ya faru ne a Kazaure da safiyar ranar 1 ga Afrilu, inda jama’a suka shiga tashin hankali da aikuwar lamarin
- Wanda aka kona ya rasu bayan an kai shi asibiti kamar yadda rahoto ya bayyana daga bakin ‘yan sanda
Jihar Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kama wani matashi mai shekara 27 mai suna Kabiru Nuhu, wanda ake zargi da kona mahaifinsa mai shekara 60 a karamar hukumar Kazaure.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Lahadi.
A cewar ‘yan sanda, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya zuba wani abu mai kama wuta, wanda ake kyautata zaton fetur ne, a jikin mahaifinsa kafin ya banka masa wuta.

Kara karanta wannan
Atiku ya gano kura kuran Tinubu a ziyarar jaje da ya kai Filato bayan an kashe bayin Allah

Source: Original
Yadda matashi ya kone mahaifinsa
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na safe a ranar 1 ga Afrilu, 2026, a unguwar Magama da ke garin Kazaure a karamar hukumar Kazaure, Punch ta ruwaito.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sanda:
“Mutumin ya kama da wuta sosai, kuma rundunar ta samu rahoto daga yankin Lokon Malamai, wanda ya sa jami’anta suka gaggauta zuwa wurin.”
Adam ya kara da cewa an kama wanda ake zargin dauke da sabbin raunukan konewa da kuma raunuka a goshinsa, hannuwansa da yatsun kafafunsa.
Meye ya faru bayan banka masa wuta?
Ya kuma bayyana cewa ana tuhumar wanda ake zargin da laifin kashe mahaifinsa, wanda babban laifi ne a dokar Najeriya.
Kakakin rundunar ya ce an garzaya da wanda aka kona asibiti, amma ya rasu yayin da ake kokarin ceto rayuwarsa.
Ya kara da cewa ana tsare da wanda ake zargin a hannun ‘yan sanda, kuma za a mika shi zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kuliya.
Shawarin kwamishinan ‘yan sandan Jigawa
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Yahaya, ya yi Allah wadai da wannan mummunan lamari, tare da tabbatar da cewa za a yi adalci.
Ya ce rundunar na ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya haddasa matashin ya farmaki mahaifinsa.
Hakazalika, ya yi kira ga jama’a da su rika warware sabani cikin lumana, sannan su rika kai rahoton duk wata alamar rikicin cikin gida ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Kira ga al’ummar Kazaure
Haka kuma, rundunar ‘yan sandan ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’anta hadin kai yayin da ake ci gaba da bincike.
Rundunar ta kuma jaddada kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar Jigawa.
A karshe, Adam ya roki duk wanda ke da wani bayani kan lamarin da ya fito ya taimaka wa jami’an tsaro domin kammala bincike.
Akan samu irin wadannan lamurra a duniya, inda 'ya'ya ke hallaka iyayensu saboda sabanin da aka samu tsakani.
Asali: Legit.ng
