Babbar Magana: Shugabannin ADC Sun Yi Taro, Sun Mika Babbar Bukata wajen INEC

Babbar Magana: Shugabannin ADC Sun Yi Taro, Sun Mika Babbar Bukata wajen INEC

  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta gudanar da taro bayan hukumar INEC ta janye amincewar da ta yi da shugabanninta
  • Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, ya bayyana cewa ba su da sauran wani kwarin gwiwa kan cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe
  • Hakazalika, Sanata David Mark, ya bayyana abin da suke son shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta mika bukatarta ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Jam'iyyar ADC ta buƙaci shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, da ya yi murabus daga muƙaminsa.

ADC ta bukaci Amupitan ya yi murabus
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

ADC ta nuna rashin gamsuwa da INEC

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban jam'iyyar ADC na kasa, David Mark, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Jam'iyyar adawa ta roki Kwankwaso, Atiku da Obi su dawo cikinta

ADC ta bayyana cewa wannan kiran ya zama dole ne saboda “shugaban hukumar da kwamishinoninsa sun nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki, don haka ba za a iya amincewa da su ba wajen gudanar da babban zaɓen 2027.”

Wace bukata ADC ta nema wajen INEC?

Sanata David Mark, wanda ya mayar da martani kan matakin janye amincewa da shugabannin ADC, ya ce jam'iyyar ba ta da sauran kwarin gwiwa kan INEC.

“Muna buƙatar murabus ɗin gaggawa ko kuma korar shugaban INEC, Farfesa Amupitan, da dukkan kwamishinonin hukumar na kasa. Ba mu da sauran kwarin gwiwa a kansu. Muna da tabbacin cewa ba su da ikon gudanar da kowane zaɓe mai sahihanci."
“Bari mu fito mu bayyana karara: za mu ci gaba da shirye-shiryen jam'iyyarmu, domin babu wani abu a ƙarƙashin doka da ya sanya halartar INEC ta zama tilas. Mun riga mun sanar da INEC kamar yadda doka ta tanada, kuma za mu ci gaba da ayyukanmu."
“Haka kuma muna kira ga kasashen duniya da su lura da matakan da INEC ta ɗauka a ranar 1 ga Afrilu, da kuma yadda muke nuna kamun kai a yau."

Kara karanta wannan

"Bai son zabe": Melaye ya fallasa abin da Tinubu yake so kan zaben 2027

"Muna roƙon su da su fahimci barazanar da ake yi wa dimokuraɗiyya da zaman lafiyar Najeriya, sannan su hukunta waɗanda ke gurgunta sahihancin tsarin zaɓe."
“Muna kiran ’yan Najeriya da su kare dimokuraɗiyyarmu. Wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci. Ku tsaya tsayin daka. Ku fito ku yi magana. Ku shiga cikin harkoki."
"Ku yi jayayya da duk wani yunƙuri na mayar da Najeriya ƙasar da ke da jam'iyya guda ɗaya kawai. Najeriya tamu ce baki ɗaya, kuma dole ne mu haɗa kai mu kare ta.”

- Sanata David Mark

ADC na neman shugaban INEC ya yi murabus
Atiku Abubakar da shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark Hoto: @atiku
Source: Twitter

Yadda ADC za ta zabi 'yan takararta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi magana kan hanyar da za ta bi wajen zabar 'yan takararta.

Jam'iyyar mai adawa a Najeriya ta bayyana cewa tana kokarin daukar tsarin maslaha wajen zabar dan takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.

Kakakin ADC na kasa ya ce jam’iyyar na da zabin gudanar da zaben kai tsaye ko kuma tsarin maslaha wajen fitar da dan takara, amma an cire tsarin zaben wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng