An Fara Maganar Gyara Tsarin Mulkin don ba Tinubu Damar Wa'adi Sama da 2

An Fara Maganar Gyara Tsarin Mulkin don ba Tinubu Damar Wa'adi Sama da 2

  • 'Yan Najeriya da dama sun taya shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 74 a duniya, inda aka masa fatan alheri game da mulkin da ya ke
  • Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi ya hararo wasu abubuwa da za su iya faruwa da ya ce za su iya jawo a nemawa Tinubu wa'adin mulki na uku
  • Oba Abdulrosheed Akanbi ya bayyana dalilan da suka sanya shi maganar a wani sako da ya fitar yana taya shugaban kasar murnar cika shekara 74

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya na iya neman a yi gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa Shugaba Bola Tinubu damar ci gaba da mulki fiye da wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun yi wa Tinubu saukar Kur'ani sama da sau 100

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi cikin saƙon taya murna da ya aikawa shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan cika shekara 74 da haihuwa.

Shugaba Bola Tinubu a ofis
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na wani jawabi. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Batun nemawa Bola Tinubu wa'adi na 3

Jaridar Punch ta rahoto cewa mai magana da yawun Oba Akanbi, Ibrahim Alli ne ya fitar da sanarwar, inda ya yabawa salon mulkin Tinubu.

“Wasu ‘yan Najeriya na iya roƙon a sake gyara kundin tsarin mulki domin Tinubu ya yi fiye da wa’adi biyu. Shi shugaba ne da ya san abin da yake yi,”

Inji shi.

Oluwo ya ce shugaban ya nuna shi na dabam ne ta hanyar yaƙi da ayyukan da ba a yi su bisa ƙa’ida ba da suka jawo koma baya ga tattalin arzikin ƙasa.

Ayyukan da ya ce Tinubu ya yi

Oba Akanbi ya ƙara da cewa ƙwarewar shugabancin Bola Tinubu ta haifar da ci gaba mai yawa, ciki har da ingantuwar darajar Naira.

The Sun ta rahoto ya ce ƙaruwar kudin ajiyar ƙasashen waje daga kusan Dala biliyan 1 zuwa tsakanin Dala biliyan 49.5 da 50.45 zuwa ƙarshen Fabrairu/Maris 2026 ya nuna kwarewar shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi abun mamaki, ya sadaukar da dukkan albashinsa na shekaru 3 ga sojoji

Sarkin ya danganta wannan ci gaban da gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da suka haɗa da haɗa tsarin canjin kuɗi, ƙara yawan man fetur da ake samarwa, da jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje.

Sarkin da ya yi wa Tinubu fatan alheri
Oba Akanbi da ya yabawa shugaba Bola Tinubu. Hoto: Emperor Abdulrasheed Adewale Akanbi Telu 1
Source: Facebook

Ya kuma yaba wa shugaban kan bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai, ƙara kaso na kuɗin da ake bai wa jihohi, faɗaɗa ayyukan tituna, da rabon tallafin gwamnati ga al’umma.

A cewarsa, shugabannin da suka gabata sun yi ƙoƙarin aiwatar da irin waɗannan gyare-gyare amma suka fuskanci matsin lamba daga jama’a da ‘yan siyasa.

'Yan fim na rikici kan Shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan fim din Hausa sun fara jifar juna da maganganu kan tallata shugaba Bola Tinubu domin ya zarce.

Sadiq Sani Sadiq ya fito a wani bidiyo yana nuna damuwa kan yadda ake cigaba da samun matsaloli a karkashin Bola Tinubu, musamman a Arewa.

Musa Mai Sana'a ya yi wa Sadiq martani mai zafi kan sukar Tinubu, lamarin da ya jawo martani daga Bello Muhammad Bello da Aminu Saira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng