Tinubu Ya Cika Shekaru 74 a Duniya, Ya Aika Muhimmin Sako ga 'Yan Najeriya

Tinubu Ya Cika Shekaru 74 a Duniya, Ya Aika Muhimmin Sako ga 'Yan Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon godiya ga daukacin 'yan Najeriya yayin da yake murnar cika shekaru 74 a duniya
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa ba zai gudanar da babban shagali a bana ba, la'akari da yanayin da kasar take ciki a yanzu
  • Tinubu ya jaddada cewa manufofin gwamnatinsa sun haifar da d'a mai ido duk da matsalolin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya janyo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tsananin godiyarsa ga 'yan Najeriya bisa dumbin saƙonni da addu'o'in da ya karɓa yayin da yake murnar cika shekaru 74 a duniya.

A cikin wani saƙo na musamman da ya fitar daga fadar shugaban ƙasa dake Abuja a yau Lahadi, Tinubu ya jinjina wa 'yan ƙasa bisa kishin ƙasa da suke nunawa.

Kara karanta wannan

Ja'oji: Ana tsakiyar taron APC, 1 daga cikin manyan hadiman Tinubu ya yi murabus

Shugaba Bola Tinubu ya aika sako ga 'yan Najeriya da ya cika shekara 74.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan wata takarda a filin Eagle Square, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya aika sakon cika shekaru 74

A sakon, wanda ya wallafa a shafinsa na X, shugaban kasar ya bayyana cewa:

"A yau, yayin da na ƙara wata shekarar a tafiyar rayuwata, na cika da farin ciki da godiya ga damar da na samu ta yi wa wannan babbar ƙasa hidima."

Shugaba Tinubu ya mika godiya ta musamman ga mai dakinsa, Oluremi Tinubu, da kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima bisa kyawawan kalaman da suka faɗa game da shi.

Ya bayyana cewa:

"Dole ne in gode wa matata, Uwargidan Shugaban Ƙasa Oluremi Tinubu, bisa irin kalaman ƙauna da ta faɗa mini, haka ma Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima."

Haka kuma, ya gode wa daukacin ƙungiyoyi da daidaikun mutane da suka biya kuɗi a gidajen rediyo da jaridu domin taya shi murnar wannan rana ta musamman yau.

Yadda Tinubu zai yi bikin murnar haihuwarsa

Daidai da al'adarsa ta kiyaye yanayin da al'umma ke ciki, shugaban ya sanar da cewa ya yanke shawarar gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa a yanayi na kankan da kai.

Kara karanta wannan

Zo ku nema: Gwamnati ta bude shafin shirin tallafa wa ƴan Najeriya miliyan 10

Tinubu ya bayyana cewa:

"Dangane da al'adata ta gudanar da ranar haihuwata daidai da yanayin da ƙasa ke ciki, na yanke shawarar gudanar da ta wannan shekarar ba tare da wani babban shagali ba."

Ya jaddada cewa wannan mataki ya zama dole domin nuna juyayi da kuma mayar da hankali kan muhimman ayyukan da suke gaban gwamnatinsa a yanzu.

Shugaban ya ƙara da cewa:

"Yayin da nake murnar wannan rana, ana tunatar da ni ƙalubalen da muka fuskanta tun lokacin da muka fara gyara-gyarenmu na tattalin arziƙi."
Shugaba Bola Tinubu ya yi godiya ga mai dakinsa Sanata Oluremi Tinubu.
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu

Shugaban ya bayyana cewa sauye sauyen da gwamnatinsa ta fara yi sun fara haifar da ɗa mai ido duk da matsalolin tattalin arziƙi da ake fuskanta a duniya.

Ya ce:

"Na yi murna cewa sadaukarwarmu ba ta tafi a banza ba, domin muna iya ganin cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, duk da tangarɗar da rikicin Gabas ta Tsakiya ya janyo."

Kara karanta wannan

Tinubu: Arewa ta Tsakiya ta gama shiri, ta fitar da 'dan takarar Shugaban kasa a 2027

Tinubu ya buƙaci 'yan Najeriya da su ci gaba da haɗa kai da gwamnatinsa domin gina ƙasar da za ta zama abin alfahari ga daukacin nahiyar Afirka.

PDP za ta goyi bayan Tinubu a 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewa zai marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake cin zaben 2027

Wani tsage na jam'iyyar PDP mai biyayya ga Wike ya fara kulla kawancen "Rainbow Coalition" domin hada kan mambobin APC da na PDP

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya nuna rashin amincewarsa da wannan mataki inda ya ce ba zai taba marawa Shugaba Tinubu baya ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com