Dan El Rufai Ya Kausasa Harshe ga Gwamna Uba Sani bayan Ya Yi Ta'aziyyar Kakarsa
- A ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026 aka sanar da rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya aika da sakon ta'aziyya ga El-Rufai kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai
- Sai dai, jim kadan bayan fitar da sakon ta'aziyyar, dan El-Rufai watau Bashir El-Rufai, ya yi masa martani mai zafi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wato Bashir El-Rufai, ya yi martani ga Gwamna Uba Sani kan ta'aziyyar rasuwar kakarsa da ya yi.
Bashir El-Rufai ya yi watsi da saƙon ta’aziyyar da Gwamna Uba Sani, ya fitar game da rasuwar kakarsa, Hajiya Umma El-Rufai.

Source: Facebook
Gwamna Sani ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris 2026 inda ya yi ta'aziyyar rasuwar Hajiya Umma El-Rufai.
Uba Sani ya yi ta'aziyyar mahaifiyar El-Rufai
Uba Sani ya nuna alhini ga tsohon gwamnan da iyalansa, inda ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kyakkyawan hali da tausayi.
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kaduna, ina miƙa saƙon ta’aziyya ga Mai girma, Mallam Nasir El-Rufai, da daukacin iyalan El-Rufai bisa rasuwar mahaifiyarsu, Hajiya Umma El-Rufai."
Ya ci gaba da yaba wa halayenta, inda ya nuna cewa ta yi rayuwa mai cike da kankan da kai da kuma hidima.
“Hajiya Umma El-Rufai ba kawai mahaifiya ce mai sadaukarwa ba, mace ce mai kwarjini, mai gaskiya, da juriya."
“Ta yi rayuwa mai cike da tausayi, kankan da kai, da kuma jajircewa wajen hidima. A cikin al'ummarta, ta kasance madogarar neman shawara da sasanci."
- Gwamna Uba Sani
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ji kan ta, Ya kuma ba wa iyalan da aka bari haƙurin jure rashin.
“Ina ta ya iyalan El-Rufai juyayi, ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya karɓi kyawawan ayyukanta, kuma Ya ba ta gida a Aljannatul Firdaus."

Kara karanta wannan
El Rufai na iya samun beli don halartar jana'izar mahaifiyarsa? Lauya ya yi bayani
- Gwamna Uba Sani

Source: Facebook
Wane martani da El-Rufai ya yi wa Uba Sani?
Sai dai kuma, yayin da yake mayar da martani ga saƙon, Bashir El-Rufai ya yi watsi da ta’aziyyar a cikin wani ɗan gajeren rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.
Bashir El-Rufai ya nuna cewa ba sa bukatar ta'aziyyar da gwamnan na jihar Kaduna ya yi musu.
“Bama so"
- Bashir El-Rufai
Kuskuren da El-Rufai ya yi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana wani babban kuskure da Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi.
Solomon Dalung ya bayyana cewa El-Rufai ya tafka babban kuskure ta hanyar miƙa kansa ga hukumomin tsaro kafin a gurfanar da shi a kotu, bayan dawowarsa Najeriya.
Duk da cewa Dalung ya kira miƙa kan da El-Rufai ya yi a matsayin kuskure, ya kuma bayyana cewa hakan ma ya zama wani tarko da El-Rufai ya dana wa gwamnatin.
Asali: Legit.ng
