Sojojin Isra'ila Sun Sha Azaba a hannun Mayakan Hezbollah, an Ji Abin da Ya Faru
- Sojojin Isra'ila na ci gaba da kutsawa Kudancin Lebanon yayin da suke fuskantar turjiya daga mayakan Hezbollah
- Mayakan Hezbollah sun harba makamai ga sojojin Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada a tsakanin bangarorin biyu
- Artabun da aka yi, ya jawo an kashe wani sojan Isra'ila mai shekara 21 yayin da aka raunata wasu da dama
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Mayakan kungiyar Hezbolla na ci gaba da fafatawa da sojojin Isra'ila a Kudancin kasar Lebanon.
An kashe sojan Isra'ila guda daya sannan wasu hudu suka jikkata a wani harin makamin fasa tanka da Hezbollah ta kai a Kudancin Lebanon.

Source: Getty Images
Jaridar The Times of Israel ta ce dakarun tsaron Isra'ila (IDF) suka sanar da hakan a yammacin ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, 2026.
'Yan Hezbollah sun kashe sojan Isra'ila

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi rashi yayin da sojojin suka gwabza da mayakan Hezbollah, Netanyahu ya shiga jimami
Kisan da mayakan na Hezbollah suka yi wa jami'in tsaron ya sa ya zama soja na biyu da ya mutu a ranar.
Sojan da aka kashe an bayyana sunansa a matsayin Sgt. Aviaad Elchanan Volansky, dan shekara 21, daga runduna ta 7th Armored Brigade’s 77th Battalion), mazaunin Kudus (Jerusalem).
Shi ne soja na hudu da aka kashe a rikicin da ake yi da Hezbollah wanda aka fara ranar 2 ga Maris 2026, lokacin da kungiyar ta Labanan ta fara harba rokoki da jirage marasa matuka kan Isra'ila a tsaka da yakin Amurka da Isra'ila da Iran.
Tun da farko a ranar, dakarun sojin sun ce an kashe wani sojan IDF a daren jiya yayin wata fafatawa da mayakan Hezbollah a Kudancin Lebanon.
Hezbollah na kai hare-hare a Isra'ila
A tsawon ranar Alhamis, hare-haren Hezbollah sun ci gaba da sauka Isra'ila, inda kungiyar ta harba rokoki fiye da 100 tare da kashe wani mutum guda da raunata wani a birnin Nahariya da ke arewacin kasar.
An ji kuwwar kararrawar gargaɗi a birnin Haifa daga baya a daren Alhamis.
IDF ta ce tankar yaki ta dakile makami guda kafin na biyu ya harbe ta
Volansky, soja na biyu da Hezbollah ta kashe a ranar Alhamis, dan babban jami'in duba ayyukan tsaro ne, Kanal Yair Volansky wanda a baya ya taba jagorantar runduna ta 401.
Bisa binciken farko na IDF, mayakan Hezbollah sun harba makaman fasa tanka guda biyu daga wani yanki da ke Arewacin kogin Litani a bangaren gabas na Kudancin Lebanon, inda suka samu wata tankar yaki ta Isra'ila nau'in Merkava.

Source: Twitter
Ministan tsaron Isra'ila ya yi ta'aziyya
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya yi ta'aziyyar sojan da aka kashe a shafinsa na X.
"Ina so na aika da saƙon ta’aziyya ga iyalan Volansky bisa rashin ɗansu, Sgt. Aviaad Elchanan Volansky, wanda ya mutu a wani yaki na gwarzantaka a Kudancin Lebanon yayin da yake kare ƙasar Isra'ila da 'yan ƙasarta."
"Marigayi Aviaad ya yi yaƙi cikin sadaukar da kai, a matsayin ɓangare na jaruman yaƙinmu waɗanda ke ɗauke da nauyin tsaron ƙasar nan a fafatawar da muke yi da maƙiyanmu."
"Na san mahaifinsa sosai, Kanal Yair Volansky, mai duba ayyukan tsaro, wanda ke aiki tare da ni kuma yake taimaka mini ƙwarai a ayyukanmu na haɗin gwiwa."
- Israel Katz
Iran ta kai hare-hare kan Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar dakarun juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da hare-hare kan Amurka da Isra'ila.
Rundunar IRGC ta farmaki muhimman cibiyoyin soja na Amurka da Isra'ila a faɗin yankin da makamai masu linzami da jirage marasa matuka.
Daga cikin wuraren da aka farmaka akwai rumbunan adana mai a Ashdod, wurin zama na ma'aikatan soja a Modi'in, da kuma cibiyar musayar bayanan sirri ta sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

