Bayan Hana Shi Hawa a Kano, Sarki Aminu Ado, Ya Aika da Sako ga Gwamna Abba

Bayan Hana Shi Hawa a Kano, Sarki Aminu Ado, Ya Aika da Sako ga Gwamna Abba

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da sallar Idi a birnin Kano a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026
  • Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kano kan su ci gaba da kokari wajen sauke nauyin da ke kansu
  • Mai martaba sarkin ya aika da sako na musamman ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bayan kammala azumin watan Ramadan

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha.

Aminu Ado Bayero ya yi kira ga gwamnatocin da su ƙara kaimi wajen kare rayuka, lafiya, da dukiyoyin 'yan ƙasa.

Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga shugabanni
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero Hoto: @HrhBayero
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Aminu Ado Bayero ya yi wannan kiran ne jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a ranar Juma'a, 20 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Bayan fiye da shekara 1, gwamnatin Kano ta waiwayi iyalan mafarautan da aka kashe a Uromi

Wane kira Aminu Ado Bayero ya yi?

Sarkin ya yaba wa gwamnatin tarayya, mambobin majalisar tarayya, da na jihohi kan tallafin da suka ba wa 'yan ƙasa a lokacin azumin Ramadan, yana mai fatan cewa za a ci gaba da yin hakan.

Kalaman Sarkin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Mai martaba Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya sanya wa hannu.

Jikan na Bayero ya jaddada buƙatar shugabanni su yi la’akari da yanayin tattalin arziki da zamantakewa da mutane ke ciki, sannan su ba wa buƙatunsu na gaggawa muhimmanci.

“Dole ne shugabanninmu su yi la’akari da ainihin yanayin da mutane ke fuskanta a halin yanzu, sannan su tabbatar da cewa kare rayuka da dukiyoyi ya kasance babban abin lura."

- Aminu Ado Bayero

Aminu Ado ya ba 'yan Najeriya shawara

Haka kuma, ya buƙaci 'yan ƙasa da su ci gaba da yi wa shugabanninsu addu’a, tare da yi masu fatan alkhairi yayin da suke gudanar da ayyukansu, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

A wani yanayi na daban, Sanusi II ya jagoranci sallar Idi a Kano, Aminu Ado ya ware a fadarsa

Bayero ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya, ci gaba, da shiriya ga shugabanni domin su magance ƙalubalen da jama’a ke fuskanta yadda ya kamata, musamman a fannonin tsaro, sauƙin farashin abinci, da samun muhimman kayayyaki.

Bugu da ƙari, ya nuna jin daɗinsa ga malaman Musulunci da limamai kan rawar da suka taka wajen yi wa muminai jagora da kuma ƙarfafa masu gwiwa kan yin ayyukan ƙwarai a duk tsawon watan azumi.

Aminu Ado Bayero ya aika da sako ga Gwamna Abba
Mai martaba Aminu Ado Bayero zaune a fadarsa Hoto: @HrhBayero
Source: Twitter

Sakon Aminu Ado ga Gwamna Abba Kabir

Sarkin ya kuma yaba wa 'yan kasuwa da masu hannu da shuni kan gudunmawar da suka bayar, tare da kira gare su da su ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da samun abinci da muhimman kayayyaki a kan farashi mai sauƙi.

Daga ƙarshe, Aminu Bayero ya taya Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, jami’an gwamnati, da al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan da bikin ƙaramar Sallah lami-lafiya.

An fadi sarkin da zai jagoranci hawa a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwa kan batun yin hawan karamar sallah na shekarar 2026.

Gwamnatin ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ne zai jagoranci wannan hawa daga filin sallar Idi na Kofar Mata.

Hakazalika, gwamnatin ta jaddada cewa ko da yake tana matukar da kiyaye wa da bunkasa al'adun Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng