"Da na Fuskanci Kaskanci," Sanusi II Ya Tuna Lokacin da Aka Cire Shi daga Sarkin Kano
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa dogaro ga Allah ya ba shi damar jure wa duk wani kunci na tsige shi daga sarauta a baya
- Mai martaba sarki Sanusi II ya jaddada cewa lokacin da ya shafe a wajen fada ya ba shi damar yin karatun digirin digirgir tare da kauce wa kaskanci
- Sarkin ya ja kunnen mutane kan kaskantar da kai ga masu iko, yana mai cewa Allah ne kadai ke bayar da mulki, ga wanda ya so, a lokacin da ya so
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon gwamnan CBN kuma sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa bai daga hankalinsa ba lokacin da ya rasa manyan muƙamai biyu mafi girma da ya taɓa riƙewa a rayuwarsa.
Sarkin ya yi bayani ne kan batun juriya da imani da ubangiji yayin da yake jawabi ga mahalarta taron bitar Ramadan na shekara-shekara na Fola Adeola.

Source: Twitter
Sarkin Kano ya fadi muhimmancin tawakkali
A wajen taron, Sanusi II ya yi tsokaci kan yadda dogaro ga Allah ya taimaka masa wajen cin jarabawar dakatar da shi a matsayin gwamnan CBN da kuma tsige shi da aka yi daga matsayin sarkin Kano, in ji rahoton Daily Trust.
Sarkin ya bayyana cewa sau da yawa mutane suna kuskure wajen jingina iko da nasara ga ’yan adam, maimakon su gane cewa lamura suna canzawa ne kawai da nufin Allah.
"A cikin rayuwarmu, muna yawan danganta abubuwa ga ’yan adam, alali kuwa su ma halittu ne," in ji Sanusi II.
Ya ƙara da cewa:
"Yakini cewa duk abin da ya yi tsanani akwai sauki a tare da shi, kuma Allah ne yake canza lamuran bawansa, yana taimaka maka wajen yin juriya da tafiyar da rayuwarka a duk halin da kake."
Haka kuma, Mai Martaba Sarki Sanusi II ya yi gargaɗi game da ƙasƙantar da kai domin neman alfarma daga wurin masu iko, yana mai nuni da cewa mutane da dama suna kuskuren tunanin cewa arziƙinsu ya dogara ne kacokan ga wasu mutane.

Kara karanta wannan
Harin tsibirin Kharg: Shugaban Amurka ya ga abin da bai yi tsammani ba a yaki da Iran
Sanusi II ya tuno lokacin da ya rasa sarkin Kano
Yayin da yake yin tsokaci game da rayuwarsa, tsohon gwamnan na CBN ya ce tafiyar rayuwarsa ta nuna yadda nasara take canzawa cikin sauri, in ji rahoton The Cable.
"An dakatar da ni daga zama gwamnan bankin ƙasa. Bayan watanni uku, na zama sarki," in ji Sarki Sanusi II.
Ya ci gaba da cewa:
"Shekaru da dama da suka wuce aka cire ni daga sarki; bayan shekaru huɗu, na dawo. Yanzu ina cikin fada ɗaya, ina kan karagar mulkina. Eh, akwai ƙalubale amma duk wanda ya dogara da Allah shi ne ke da nasara. Babu wata fargaba."

Source: Twitter
Rayuwar Sanusi II bayan barin fadar Kano
Sarki Sanusi II ya bayyana cewa lokacin da ya shafe a wajen Kano bayan tsige shi daga sarauta, ya ba shi damar guje wa wasu yanayi da za su iya zama na wulaƙanci, sannan ya ba shi damar ci gaba da karatunsa na ilimi.
Sarkin ya ce:
"Ina tunanin duk abubuwan da za su iya faruwa idan ina Kano a shekaru huɗun da suka gabata, ƙasƙancin da zan iya fuskanta, mutanen da zan riƙa mu'amala da su, da mutanen da zan riƙa kai wa rahoto, amma Allah Mai jin ƙai ne, Mai rahama ne. Ya fitar da ni daga wannan yanayin. Ya ba ni dama, na je na yi digirin digirgir, sannan na dawo."
Sanusi ya yi aiki a matsayin Gwamnan CBN daga shekarar 2009 zuwa 2014. Gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ce ta tsige shi daga sarkin Kano a shekarar 2020, kafin gwamna mai ci yanzu, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da shi kan karaga a shekarar 2024.
Sarki Sanusi II ya yi shiga ta musamman
A wani labari, mun ruwaito cewa, Mai martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya sauya tufafi yayin zaman fada a ranar 20 ga watan Ramadan 1447.
Sanarwar da Legit Hausa ta samu daga masarautar ya nuna cewa Sarki Sanusi II ya yi shigar ne domin tunawa da tarihin Musulunci.
An ce sanya bakin rawani na cikin al'adar Sarkin a ranar 20 ga Ramadan domin tunawa da wata nasarar da Annabi Muhammad SAW ya samu.
Asali: Legit.ng


