'Yan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Daruruwan Mutane bayan Kai Hari a Borno

'Yan Boko Haram Sun Yi Awon Gaba Daruruwan Mutane bayan Kai Hari a Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun kashe jami'am sojoji tare da fararen sallah kafin daga bisani su sace wasu mutanen zuwa cikin daji
  • Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana cewa akwai daruruwan mutane da ba a san inda suke ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne sun yi garkuwa da fiye da mazauna 300 a garin Ngoshe yayin wani mummunan hari da suka kai a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Wannan hari ya tilasta wa dubban mutanen da suka tsira tserewa zuwa garin Pulka, inda da yawa daga cikinsu ke kwana a kan tituna da cikin gine-ginen makarantu saboda tsoron sake aukuwar wani harin.

Kara karanta wannan

An nemi Na'ibin limami da wasu mazauna Katsina an rasa bayan hare haren yan ta'adda

'Yan Boko Haram sun sace mutane a Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum Hoto: @GovZulum
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe adadin fararen hula da ba a tantance ba.

'Yan Boko Haram sun sace mutane a Borno

'Yan ta'addan sun kuma yi garkuwa da mata da dama bayan kaddamar da hari kan wani sansanin sojoji a yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari ne kan sansanin sojoji da ke Ngoshe kafin su lallaba su fada wa mazauna garin da misalin ƙarfe 1 na daren Laraba, 4 ga watan Maris 2026.

Shaidun gani da ido sun ce harin ya ɗauki sa’o’i da dama, inda ya bar tsoro da barna, kafin a tura dakarun sama na Operation Hadin Kai domin fatattakar maharan zuwa cikin daji.

A cewar rahotanni na ranar Alhamis, sojojin Najeriya sun kashe ɗinbin ’yan ta’addan Boko Haram bayan harin da suka kai wa sansanin sojin na Ngoshe, wanda aka bayar da rahoton cewa ya yi sanadin mutuwar sojoji tara.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya, sun yi wa limamin masallaci yankan rago

Bayan farmakin, jiragen leƙen asiri sun bi sawun mayakan tare da kai musu harin bam, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mayaka 50.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da aukuwar harin.

Ya kara da cewa hukumomi na nan suna aiki don tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su.

“Harin ya shafi wasu fararen hula da ba a tantance adadinsu ba. Wasu da dama har yanzu ba a gansu ba, kuma ana fargabar an yi garkuwa da su an nufi tsaunukan Mandara da su."
“Ya zuwa yanzu, ba mu kammala tantance jimillar waɗanda aka tafi da su ba. Idan rahotannin cewa Babban Limamin garin ma ba a ganshi ba sun tabbata, za mu tabbatar mu sanar da ku."

- Nahum Kenneth Daso

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, domin bai ɗaga kiran wayar da aka yi musu ba.

'Yan Boko Haram sun sace mutane a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ndume ya ce mutane da dama sun bace

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shammaci 'yan sanda ana azumi, sun yi barna mai girma

Jaridar Daily Trust ta ce Sanata mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi Allah wadai da harin yayin wata hira da manema labarai ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa fiye da mazauna garin 100 har yanzu ba a gansu ba.

A cewar sanatan, mayakan sun mamaye sansanin sojoji ne a Ngoshe kafin su kaddamar da farmaki kan al'ummar garin.

"Fiye da mutane 100 ne har yanzu ba a gansu ba ko kuma an yi garkuwa da su yayin harin, yayin da dubban fararen hula, waɗanda yawancinsu mata ne da ƙananan yara, suka rasa matsugunansu kuma a halin yanzu suna gudun hijira a garin Pulka."

- Sanata Ali Ndume

'Yan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a sansanin sojoji da ke Borno.

'yan ta’addan Boko Haram sun kashe kwamandan sansanin sojoji na FOB wanda yake babban jami’i ne mai muƙamin Manjo.

Tsagerun 'yan ta'addan sun kuma kashe sojoji uku da kuma mafarauci ɗaya yayin wani mummunan hari da suka kai wa sansanin sojojin da ke Mayanti, a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng