'Yadda Shugaba Tinubu Ya Hana Trump Kawo Farmaki don Mamaye Najeriya'
- A kwanakin baya Shugaba Donald Trump na Amurka ya matsawa Najeriya lamba kan zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi
- Issa Aremu wanda ke shugabantar wata cibiya a Ilorin, ya yabawa Bola Ahmed Tinubu kan rawar da ya taka wajen yayyafawa wutar ruwan sanyi
- Ya bayyana cewa da ba domin kokarin da Shugaba Tinubu ya yi ba, da abubuwa ba su yi wa Najeriya kyau ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - Shugaban cibiyar nazarin harkokin kwadago ta Michael Imodu (MINILS) da ke Ilorin, Issa Aremu, ya yaba kan rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka yayin takaddama da Amurka kan zargin kisan Kiristoci.
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da dabarun diflomasiyya wajen shawo kan takaddama tsakaninsa da takwaransa na Amurka, Donald Trump, kan zargin kisan kare-dangi ga Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Maris 2026 yayin taron bita na Ramadan karo na biyar na cibiyar mai taken "rawar da musulmi za su taka wajen taimaka wa masu karamin karfi," wanda al'ummar Musulmi na cibiyar suka shirya.
Wane kokari Shugaba Bola Tinubu ya yi?
Ya bayyana cewa dabarun diflomasiyyar da Tinubu ya yi amfani da su, sun hana Amurka mamaye kasar nan.
A cewarsa, maimakon Shugaba Tinubu ya shiga tattaunawa a fili ko musayar kalamai na batanci, ya amince da yin amfani da dabarun diflomasiyya na natsuwa amma masu karfi domin kwantar da tarzoma.
"Shugaba Tinubu ya nuna natsuwa sannan ya yi aiki a bayan fage domin lallashinsa (Trump) ya janye."
"Shugaba Tinubu ya yi amfani da diflomasiyya ne domin hana Trump kai wa Najeriya hari a kan wani zargin kisan kare-dangi na banza wanda ba shi da tushe."
- Issa Aremu
Tinubu ya yi dabara wajen warware zargin Amurka
Ya kafa hujjar cewa idan da Shugaba Tinubu ya mayar da martani na fada, da takaddamar ta karu wanda hakan zai haifar da mummunan sakamako, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
"Idan da Shugaba Tinubu bai yi amfani da diflomasiyya a wannan lamari ba, watakila da yanzu muna farmakar juna. Da yanzu watakila muna kashe kanmu."
Issa Aremu
Ya ba da shawara kan warware rikice-rikice
Haka kuma, Issa Aremu ya yi kira da a yi amfani da tattaunawa ta diflomasiyya wajen warware rikice-rikicen kasa da kasa, ciki har da takaddamar da ke tsakanin Amurka da Iran.
"Gara a yi ta magana da baki da a yi yaki saboda sakamakon da hakan ke haifarwa, musamman ga iyalai wadanda suke asarar masoyansu."
- Issa Aremu

Source: Twitter
Shugaban cibiyar ya bukaci 'yan Najeriya da kada su fidda tsammani duk da kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan kasar.

Kara karanta wannan
Trump ya fadi adadin shugabannin Iran da aka kashe, ya bayyana mamakin da kasar ta ba shi
Tsohon shugaban na NLC ya jaddada muhimmancin tattaunawa da zaman lafiya wajen warware rikici, na cikin gida ne ko na kasashen duniya.
Bola Tinubu ya nada shugaban NSCDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NSCDC.
Mai girma Bola Tinubu ya sabunta wa'adin Dr. Ahmed Abubakar Audi, a shugabancin hukumar NSCDC ta kasa.
Sabunta wa'adinsa na sa na shekara biyar na zuwa ne bayan ya ajiye aiki sakamakon cikar wa'adinsa na farko wanda aka nada shi a shekarar 2021.
Asali: Legit.ng

