Jihar Kano Ta Yi Babban Rashi ana Azumi, Tsohon Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- An shiga jimami a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma bayan rasuwar daya daga cikin tsofaffin kwamishinonin da suka yi aiki a gwamnati
- Tsohon kwamishinan kudi a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Kabiru Dandago, ya koma ga mahaliccinsa
- Farfesa Kabiru Dandago ya yi aiki a jami'ar Bayero da ke Kano kafin rasuwarsa kuma ya ba da gudunmawa sosai a fannin ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - An yi babban rashi a jihar Kano, na tsohon kwamishina, Farfesa Kabiru Isa Dandago, wanda ya koma ga mahaliccinsa.
Farfesa Kabiru Isa Dandago ya kasance tsohon kwamishinan kudi a lokacin da Abdullahi Umar Ganduje ke mulkin jihar Kano.

Source: Twitter
Jaridar Aminiya ta kawo rahoton cewa tsohon kwamishinan kudin ya rasu ne a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, 2026.
Tsohon kwamishina a Kano ya rasu
Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke cikin birnin Kano da yammacin ranar Laraba.
Daraktan yaɗa labarai na jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Lamara Garba, ya tabbatar da rasuwar marigayin wanda ya kasance farfesa.
Farfesa Kabiru Dandago ya koyar da lissafin kuɗi da haraji a tsangayar ilimin zamantakewa da gudanarwa ta jami'ar BUK.
A wane lokaci ya rike mukamin kwamishina?
Marigayin ya yi aiki a matsayin kwamishinan kuɗi na jihar Kano daga watan Yunin 2015 zuwa Oktoban 2018 a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Farfesa Kabiru Dandago ya fara aiki a jami’ar Bayero a watan Satumban 1990, kuma daga baya ya zama shugaban tsangayar ilimin zamantakewa da gudanarwa.
A tsawon lokacin da ya kwashe yana aiki, Farfesa Kabiru Dandago ya rubuta tare da gyara littattafai da dama kan nazarin kuɗi, haraji, kuɗi da tattalin arziƙi.
Jami'ar BUK ta yi ta'aziyya
Jami'ar BUK ta yi ta'aziyyar rasuwar tsohon kwamishinan na kudi a jihar Kano wanda ya yi bankwana da duniya.
A cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X, jami'ar BUK ta yi addu'o'in samun rahamar Allah ga marigayin.

Source: Original
Sanarwar na cewa:
"Tare da cikakkiyar miƙa wuya ga hukuncin Allah Maɗaukakin Sarki, muna sanar da rasuwar Farfesa Kabir Isa Dandago."
"Ya rasu ne a yau Laraba, 4 ga watan Maris, 2026, a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH). Marigayin ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano."
"A madadin shugabanni, ma'aikata, da ɗalibai, muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga iyalansa. Muna roƙon Allah ya ji ƙansa da rahama."
Basarake ya rasu a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi rashi na daya daga cikin sarakunan da ake da s. A jihar Osun da ke Kudancin Najeriya.
Sarkin Ikire da ke jihar Osun, Oba Olatunde Falabi, ya riga mu gidan gaskiya, yana da shekaru 91 a duniya.
Oba Olatunde Falabi wanda kwararren masanin harkokin magunguna ne, an nada shi a matsayin Akire na Ikire a watan Mayu 1993, inda ya yi sarauta sama da shekaru 30.
Asali: Legit.ng

