Abin da Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabon Shugaban 'Yan Sanda yayin Rantsar da Shi
- Olatunji Disu ya zama sabon mukaddashin shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya bayan nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin wanda zai jagoranci ragamar rundunar 'yan sandan Najeriya
- Mai girma Bola Tinubu ya bukaci Olatunji Disu da ya dawo da zaman lafiya tare da karfafa tsaro a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da mukaddashin sabon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bukaci Olatunji Disu, da ya maido da zaman lafiya tare da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa kan tarihin aikinsa da kwarewarsa.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya ba da wannan umarni ne a fadar shugaban kasa yayin taron rantsar da Olatunji Disu a matsayin mukaddashin IGP, a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026, kamar yadda Bayo Onanuga ya sanya a shafinsa na X.
Nadin Olatunji Disu dai ya biyo bayan yin mirabus din da Kayode Egbetokun ya yi daga mukaminsa na shugaban 'yan sanda.
Tinubu ya san Olatunji Disu
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya san tarihin aikin Olatunji Disu a rundunar 'yan sandan Najeriya.
“Na yanke wannan shawarar ne domin ka ɗauki wannan nauyin jagorancin. Na san tarihin aikinka. Na ga irin jajircewar da ka nuna lokacin da kake Legas sannan ina kan kujerar gwamna."
- Shugaba Bola Tinubu
Me Tinubu ya gayawa sabon IGP?
Ya bayyana cewa naɗin ya zo ne a wani mawuyacin lokaci, inda ya buƙaci sabon shugaban ’yan sandan da ya sake gina amincewar jama’a ga rundunar, sannan ya yi aiki kafa-da-kafa da sauran hukumomin tsaro.
“Ka yi jagoranci cikin tsayin daka amma tare da adalci, ka bukaci kwarewa a kowane mataki, sannan ka tabbatar da amincin rayuka da dukiya ya kasance babban abin da muka sa a gaba."
"Wannan babban ƙalubale ne. Na san za ka iya. Ina ba ka amincewata, kuma ina ba ka cikakken goyon baya."

Kara karanta wannan
Babu wasa: Sabon shugaban 'yan sanda ya sanar da 'yan Najeriya shirinsa bayan fara aiki
“Najeriya tana fuskantar ƙalubalen 'yan bindiga, ta’addanci, da sauran ayyukan laifuffuka. Za ka kasance ɓangare na masu tunani da kawo sababbin dabarun shawo kansu."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya yabawa Egbetokun
Haka kuma, Tinubu ya jinjina wa tsohon shugaban ’yan sandan da ya yi ritaya, Kayode Egbetokun, wanda ya halarci taron tare da mai ɗakinsa.

Source: Twitter
“Ga shugaban ’yan sanda mai barin gado, mu al’umma ce mai godiya a gare ka. Najeriya tana jin daɗin gudunmawarku wajen tabbatar da doka da oda."
- Shugaba Bola Tinubu
Ya bukaci Egbetokun da ya ci gaba da ba wa rundunar goyon baya ta hanyar ba wanda ya gaje shi shawara.
“Ba ka yi nasara ba idan babu wanda ya gaje ka na gari. Nasararsa za ta kasance ɓangare na abin da za a tuna da kai da shi."
- Shugaba Bola Tinubu
Shirin sabon shugaban 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon mukaddashin shugaban 'yan sanda, Olatunji Disu, ya bayyana shirin da yake da shi.
Olatunji Disu ya bayyana cewa zamanin yin ba dai-dai da kuma rashin bin doka a rundunar ’yan sandan Najeriya ya zo karshe.
Hakazalika, ya ba da tabbacin cewa zai horar da jam'ian 'yan sanda tare da karfafa gwiwarsu wajen ganin sun kiyaye hakkokin ɗan adam.
Asali: Legit.ng
