Zance Ya Fito: ICPC Ta Yi Magana kan Batun El Rufai Ya Shiga Mummunan Hali a Hannunta
- Mai magana da yawun bakin Nasir Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa tsohon gwamnan Kaduna ya fuskanci matsalar rashin lafiya yayin da yake tsare a hannun ICPC
- Muyiwa Adekeye ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan ya rika zubar da jini ta hancinsa yayin yake tsare a hannun ICPC kan wasu zarge-zarge
- Sai dai, hukumar ICPC ta hannun kakakinta ta yi magana kan ikirarin da aka yi kan lafiyar tsohon gwamnan na Kaduna
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta yi magana kan batun cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu matsala yayin da yake tsare a hannunta.
Hukumar ICPC ta musanta iƙirarin da ake yi na cewa Nasir El-Rufai, ya fuskanci matsalar zubar jini ta hanci lokacin da yake tsare a hannunta.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce hukumar ICPC ta mayar da martani ne ga zarge-zargen da kakakin El-Rufai, Muyiwa Adekeye ya yi.
Muyiwa Adekeye dai ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan ya fuskanci matsalar lafiya lokacin da yake tsare a hannun hukumar ICPC.
Me ICPC ta ce kan rashin lafiyar El-Rufai?
Kakakin hukumar ICPC, Okor Odey, ya karyata wannan zargi a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2026, jaridar The Guardian ta kawo labarin.
“Zargin da ake yi na cewa El-Rufai ya zubar da jini daga hancinsa jiya lokacin da yake tsare a hannun ICPC ba gaskiya ba ne."
- Okor Odey
El-Rufai yana tsare a hannun ICPC tun ranar 18 ga Fabrairu, bayan sakin sa da Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziƙi Ta’annati (EFCC) ta yi, inda ya kwashe dare biyu a hannunta.
Hadimin El-Rufai ya yi zarge-zarge
Adekeye ya yi iƙirarin tun da farko cewa ba a nuna wa lauyoyin El-Rufai wani umarnin kotu da ke ba da ikon ci gaba da tsare shi ba bayan cikar sa’o’i 48 ba tare da an shigar da ƙara ba.
Haka kuma, ya yi iƙirarin cewa iyalan tsohon gwamnan suna fuskantar matsaloli wajen ganinsa a inda ake tsare da shi.
“Ba a bar daya daga cikin matansa ta kai masa abincinsa kai-tsaye ba a yammacin ranar 17 ga Fabrairu, inda aka buƙaci ta bayar ta hannun ɗaya daga cikin jami’an hukumar."
"Lauyoyinsa sun ba da rahoton cewa ya fuskanci matsalar zubar jini daga hanci a cikin dare."
- Muyiwa Adekeye

Source: Twitter
ICPC, EFCC na bincikar El-Rufai
Hukumomin ICPC da EFCC suna binciken El-Rufai ne kan zargin rashin gaskiya a harkar kuɗi lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan Kaduna tsakanin 2015 zuwa 2023.
A shekarar 2024, majalisar dokokin jihar Kaduna ta tuhumi tsohon gwamnan kan zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a har Naira biliyan 432 da kuma safarar kuɗaɗen haram, inda ta ba da shawarar a gurfanar da shi.
An samu tsaiko a shari'ar El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an dage lokacin gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kaduna, zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026.
Hukumar DSS ce dai ta shigar da kara kan tsohon gwamnan na Kaduna a gaban inda take yi masa tuhume-tuhume guda uku.
Asali: Legit.ng


