An Yi Babban Rashi: Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda a Najeriya Ya Rasu

An Yi Babban Rashi: Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda a Najeriya Ya Rasu

  • Mutuwa mai yankar kauna ta ratsa rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na tarayyar Najeriya
  • Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar Borno da ke aiki a sashen binciken manyan laifuffuka, Abubakar Balteh, ya koma ga mahaliccinsa
  • Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da rasuwar marigayin, inda ta bayyana musabbabin rasuwarsa a cikin wata sanarwa da ta fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta yi rashi na daya daga cikin manyan jami'anta.

Mataimakin kwamishinan ’yan sanda (ACP) na sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar, ACP Abubakar Balteh, ya riga mu gidan gaskiya.

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan Borno ya rasu
Marigayi mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Borno, Abubakar Balteh Hoto: Nahum Daso Kenneth
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata gajeriyar sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Nahum Daso, ya fitar a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

APC ta sha kasa: INEC ta sanar da sakamakon zaben ciyaman da aka gudanar a Abuja

Rundunar 'yan sanda ta yi rashi

ASP Nahum Daso, ya bayyana cewa ACP Abubakar Balteh ya rasu ne a ranar 21 ga Fabrairu, 2026, sakamakon wani mummunan hatsarin mota.

"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN"
"Rundunar ’yan sandan jihar Borno na baƙin cikin sanar da rasuwar ACP Abubakar A. Balteh, wanda ya riga mu gidan gaskiya a yau, 21 ga Fabrairu, 2026, sakamakon wani mummunan hatsarin mota."
"Har zuwa lokacin rasuwarsa, ya yi aiki cikin kwazo a matsayin mataimakin kwamishinan ’yan sanda na sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) na rundunar jihar Borno."

- ASP Nahum Daso

Za a sanar da lokacin jana'iza

ASP Nahum Daso ya bayyana cewa za a sanar da cikakkun bayanai game da shirye-shiryen jana’izarsa da sauran bayanan da suka shafi hakan nan gaba kadan.

"Za a sanar da cikakkun bayanai game da shirye-shiryen jana’izarsa da sauran bayanai masu alaƙa a lokacin da ya dace."
"Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma ji kansa da rahama."

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

- ASP Nahum Daso

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya yi bankwana da duniya a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani ACP ya taba rasuwa a Borno

Idan za a iya tunawa, a watan Nuwamba na shekarar 2025, ASP Nahum Daso ya taba sanar da rasuwar mataimakin kwamishinan ’yan sanda (DCP) na sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar, DCP Ahmed Ibn Umar, wanda ya rasu bayan ya yi fama da jinya.

A waccan lokacin, jami’in hulda da jama’ar na rundunar 'yan sandan jihar Borno ya ce:

“Rundunar ’yan sandan jihar Borno na baƙin cikin sanar da rasuwar DCP Ahmed Ibn Umar, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH) bayan ya yi fama da jinya.”
“Ya yi aiki cikin kwazo a matsayin mataimakin kwamishinan ’yan sanda na sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) na rundunar jihar Borno. Allah ya jikansa da rahama.”

Sanata Barinada Mpigi ya bar duniya

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najetiya ta yi rashi na daya daga cikin sanatocin da take da su

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke mai kawo ga 'yan ta'adda, an kashe kwamandan Boko Haram

Sanatan da ke wakiltar mazabar Rivers ta Kudu maso Gabas a majalisar dattawan Najeriya, Barinada Mpigi, ya yi bankwana da duniya.

Barinada Mpigi, wanda shi ne shugaban kamitin majalisar dattawa kan ayyuka, ya bar dunya ne yana da shekaru 64 bayan ya sha fama da rashin lafiya na wani lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng