Tinubu Ya Zalunci Musulmai: Sheikh Yakubu Katsina Ya Soki Gwamnati a Wurin Tafsiri
- Daraktan kungiyar Izala a Najeriya, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya bayyana rashin jin dadinsa da mulkin shugaba Tinubu
- Shehin ya zargi Tinubu da zaluntar Musulmai a Najeriya, ya yi kira da a gaggauta kwatowa Musulmai ‘yancinsu
- Ya kuma bayyana rashin gamsuwa da yadda gwamnatin ta zo da tsarin haraji mai kama da na Yahudawa a kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Jihar Katsina - Sheikh Yakubu Musa Hassan Sautus Sunnah, daya daga manyan shugabannin kungiyar Izala a Najeriya ya fito don nuna fushi da rashin gamsuwa da tsarin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shehin Malamin ya bayyana karara cewa, lallai Shugaba Tinubu ya zalunci Musulmin Najeriya, kuma lallai wannan abin lura ne da mai da hankali a kai.
Wannan na fitowa ne daga bakin malamin a wani bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta na lokacin da malamin ke tafsirin watan Faburairun Ramadan a 2026.

Source: UGC
Sheikh Yakubu ya tura sako ga makusantan Tinubu Musulmai
A bidiyon, malamin ya fito karara ya nemi dukkan wadanda ke tare da Tinubu kuma Musulmai da su tabbatar sun kwatowa Musulmai ‘yancinsu.
Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya zalunci Musulmai, don haka hakkinsu ya kamata ya fito cikin gaggawa.
A cewarsa:
“Ina kira ga dukkan jami’an da ke cikin gwamnatin nan, kuma suna Musulmi da su tsaya lallai su kwatowa al’ummar Musulmi ‘yancinsu. Tinubu ya zalunce mu.”
Ba mu yarda da batun harajin Tinubu ba, Sheikh Yakubu
Da yake tsokaci kan yadda gwamnatin Tinubu ta kawo tsarin haraji, ya ce sam Musulmai ba su gamsu da haka ba.
Hakazalika, ya koka kan yadda ‘yan kasar ke shan wahalar samun abincin da za su ci, ga kuma batun Karin haraji da aka kawo.
Ya kara da cewa:
“Sannan maganr haraji, muna kira ga ‘yan majalisa har yanzu ba mu yarda dashi ba. Wannan tsarin haraji na Yahudanci ba mu yarda da shi ba.”
Allah ya ba mu arziki, a ba mu hakkinmu, Sheikh Yakubu
Da yake magana kan irin arzikin da Allah ya yiwa kasar, Shehin Malamin ya ce akwai bukatar gwamnati ta cire albarkatun da Allah ya bai wa kasar domin talaka ya ji dadi.
Hakazalika, ya jaddada rashin gamsuwa da karbar kudade a hannun ‘yan Najeriya da sunan harajin da malamin ya ce tsari ne na Yahudawa.
Ya ce:
“Allah ya azurta mu Najeriya da arziki a karkashin kasa ba man fetur kadai ba, ka ajiye shi a gefe guda. Gwamnati ki zo ki tono a saida a ba mutane arzikin da Allah ya ba su.
“Sai ka zo kana bin talakawa masu fama da ina za su sami abincin da za su ci kana cewa su ba da haraji, komai karancin abu wai sai an cire haraji.”
Kungiyar Izala bata yarda da tsarin Tinubu ba, Sheikh Yakubu
A kalaman nasa, malamin ya ce wadannan kalamai ya yi su ne a matsayinsa na babba a kungiyar Izala mai yada addinin Islama a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa, yana da matsayi a kungiyar, don haka yana da ikon fada a ji a kungiyar mai miliyoyin mabiya a nahiyar Afrika.
A cewarsa:
“To muna kira da babban murya da sunan kungiiyar Izalatul Bidi’a wa Ikatamtus Sunnah, kun san ni waye a Izala ai.”
Sheikh Yakubu Musa ne daraktan kungiyar izala ta tarayyar Najeriya, kuma yana daga cikin wadanda suke wa’azi a kasar nan a karkashin kungiyar.
Asali: Legit.ng

