Ramadan: Dakarun Hisbah Sun Cafke Gandaye da Rana Gotai Gotai a Kano
- Dakarun hukumar Hisbah sun yi nasarar kama wasu mutane da aka da yakinin gandaye ne yayin da Musulmi ke yin azumi
- Hukumar ta bayyana takaicin a kan yadda Musulmi zai rika cin abinci gatsal-gatsal yayin da takwarorinsa ke azumtar Ramadan
- Mataimakin kwamandan hukumar, Mujahid Aminudeen ya bayyana cewa irin matakin da aka dauka, kuma za a dora su a hanya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta yi nasarar kama Musulmai tara a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu, 2026 wanda ya zo dai-dai da 2 ga watan Ramadan 1448 bayan hijira.
Jami'an hukumar sun yi ram da mutanen ne bayan an gan su suna cin abinci a ranar farko ta azumin bana na Ramadan.

Source: Facebook
BBC ta wallafa cewa Kano jiha ce mai yawan al’ummar Musulmai, inda ake gudanar da tsarin shari’ar Musulunci tare da kundin tsarin mulkin kasa.
Gandaye 9 na hannun Hisbah a Kano
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mataimakin kwamandan hukumar, Mujahid Aminudeen ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama, akwai maza bakwai da mata biyu.
Ya ce jami’an Hisbah sun dauki matakin ne bayan samun rahoton cewa mutanen sun karya dokar azumi da gangan, duk da cewa an dauki azumi.
A cewarsa:
“Za mu ilmantar da su kan muhimmancin azumi da yadda Musulmi ya kamata ya rayu cikin gaskiya da rikon addini.”
Hisbah za ta yi wa gandaye wa'azi
Malam Muhajid Aminudeen ya kara da cewa a halin yanzu mutanen na tsare a hannun hukumar, inda jami’ai ke shirin yi masu nasiha.

Source: Facebook
Za a tunatar da su a kan darajar azumi a addinin Musulunci da kuma yadda ya kamata su kiyaye ibadu kamar sallah da karatun Alkur’ani.
Ya bayyana cewa manufar hukumar ba wai hukunci ba ne kawai, illa ma gyara jama'a da fadakarwa domin su zama Musulmai nagari masu bin dokokin addini yadda ya dace.
Yaushe Hisbah za ta saki wadanda aka kama?
Sai dai Mataimakin kwamandan bai fayyace lokacin da za a sako wadanda aka tsare ba. A al’adar hukumar, ana kan tuntubar iyalan wadanda aka kama domin tabbatar su saka ido a kansu.
Hukumar Hisbah a Kano kan gudanar da sintiri na musamman a duk lokacin Ramadan, inda take duba gidajen abinci da kasuwanni domin tabbatar da cewa Musulmai suna bin ka’idojin azumi.
Wannan na daga cikin matakan da ake dauka domin kare martabar watan mai alfarma da kuma tabbatar da bin tsarin Shari’a a jihar da Musulmi suka fi rinjaye.
Ramadan: Abba ya yi wa ma'aikata gata
A baya, kun samu labarin cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da rage sa’o’in aiki ga ma’aikatan gwamnati domin saukaka masu.
Rahotanni sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne a matsayin wata hanya ta karrama ma’aikata tare da ba su damar gudanar da ibadunsu cikin sauki.
Saukaka wa ma'aikatan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 18 ga Fabrairu, 2026, wadda ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar ya fitar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


