'Yan ISWAP Sun Yi Rashin Kunya, Sun Kutsa Sansanin Sojojin Borno Sun Yi Barna
- ‘Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kai wani mummunan hari a kan sansanin sojoji da ke jihar Borno inda suka yi barna mai yawan gaske
- Rahotannin da aka samu zuwa yanzu sun tabbatar da cewa sojoji takwas sun mutu, 23 sun jikkata a harin da ya gigita na kusa da yankin
- Maharan, wadanda suka yi jeron gwano a kan babura akalla 70, sun kurda ta hanyoyi daba-daban kafin su isa sansanin da aka kai wa hari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Sojojin Najeriya akalla takwas sun rasa rayukansu yayin da wasu 23 suka jikkata sakamakon wani hari da ‘yan ta’addan ISWAP a Borno.
An ce kimanin mayaƙan ISWAP 70 wadanda suka zo a kan babura, sun kai farmaki sansanin sojoji da ke kauyen Cross Kauwa a Borno a ranar Litinin.

Source: Original
Daily Trust ta ruwaito rahotanni daga majiyoyin tsaro uku sun tabbatar da cewa harin ya janyo mummunar musayar wuta tsakanin sojojin da maharan.
Maharan ISWAP sun kai hari Borno
Wani jami'in soja da ya nemi a sakeye sunansa ya tabbatar da harin da ya salwantar da rayuka mutum takwas daga bangarensu.
Ya ce:
“Sojoji takwas sun rasa rayuwarsu, yayin da wasu 23 suka samu raunuka.”
Majiyoyi biyu daga ‘yan sa-kai masu yaki da ta’addanci da ke taimakawa sojoji sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu da jikkata.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun taso ne daga sansaninsu da ke tsibirin Dabar Masara a Tafkin Chadi.
Yadda maharan ISWAP suka shiga sansanin sojoji
Rahotanni sun ce maharan sun bi wata doguwar hanya domin kai wa sansanin harin ba-zata ba tare da an hango su da wuri ba.

Source: Twitter
Wani dan sa-kai ya ce maharan sun kona sansanin gaba daya tare da lalata motoci 11 na yaki dauke da manyan bindigun kariya daga jiragen sama, sannan suka kwashe makaman.
Sansanin da aka kai wa hari yana tazarar kilomita 24 daga garin Baga, wanda ya shahara a harkar kamun kifi.
Kungiyar ISWAP da kuma abokiyar hamayyarta Boko Haram sun kara kaimi wajen kai hare-hare kan sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.
A karshen makon da ya gabata, an kai hare-hare biyu a Borno, inda aka kashe tare da jikkata sojoji da ‘yan sa-kai.
A daren Asabar 14 ga watan Fabrairu, 2026, ISWAP ta kai hari a Mandaragirau kusa da dajin Sambisa, inda aka samu asarar rayuka, a cewar sanarwar rundunar soji.
ISWAP ta kuma kai hari Borno
A wani labarin, mun wallafa cewa 'yan ta'adda ISWAP sun sake kai hari garin Mayenti a Bama da ke jihar Borno, inda hallaka wasu 'yan sa-kai huɗu.
Rundunar Operation Hadin Kai ta yi artabu da mayakan a harin ya zo bayan ISWAP ta saki bidiyon kashe Birgediya Janar M. Uba Harin ya kara tayar da hankalin jama’a.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa harin ya faru a daren Litinin, inda mayakan ISWAP suka kutsa cikin garin cikin daruruwan babura suka bude wa bayin Allah wuta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

