"Babu Ruwan DSS," An Ji Wadanda Suka Cafke El Rufai bayan Ya Bar Hannun EFCC
- Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na hannunta bayan EFCC ta sake shi a daren Laraba
- Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da suka yi ikirarin cewa El-Rufai ya fada hannun jami'an DSS bayan ya samu beli daga EFCC
- A ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026, babban jagoran na ADC ya amsa gayyatar EFCC awanni kadan bayan dawowarsa Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya koma hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.
Malam Nasir El-Rufai, wanda ya shafe sa’o’i 48 a hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'adi (EFCC), an sake kama shi ne bayan ya samu beli a daren jiya Laraba.

Source: Twitter
Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa El-Rufai na hannunta a wata gajeruwar sanarwar da ta wallafa a shafinta na X
Malam El-Rufai ya amsa gayyatar EFCC ne a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026, kuma bayan shafe kwanaki biyu, aka mika shi ga ICPC.
El-Rufai: Zargin DSS da ƙarar da ta shigar
Da farko, wasu rahotanni sun nuna cewa jami’an hukumar DSS ne suka kama shi bayan ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja tun lokacin da yake EFCC.
DSS ta shigar da tuhuma kan tsohon gwamnan bisa zargin sa da hannu a kutse tare da sauraron wayar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu.
Hukumar ICPC ta tsare El-Fufai a Abuja
Sai dai daga baya ICPC ta fayyace cewa El-Rufai na hannunta ne, ba hannun DSS ba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A cewar J. Okor Odey, Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na ICPC, sun karɓi El-Rufai a daga hannun hukumar EFCC a daren Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, domin ci gaba da bincike. Sai dai bai bayyana takamaiman abin da ake bincike a kai ba.

Source: Twitter
Yunƙurin kama El-Rufai a filin jirgi
A makon da ya gabata, jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe bayan dawowarsa daga birnin Alkahira na ƙasar Masar.
A wata hira da aka yi da shi, Malam Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa ICPC, bisa umarnin NSA, ta buƙaci DSS ta kama shi.
Da aka tambaye shi ta yaya ya san hakan, ya ce wani ya saurari wayar Ribadu kuma ya ji abin da ya faɗa.
Yadda El-Rufai ya yi kwana 2 a EFCC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya sake kwana a hannun hukumar EFCC yayin da ake gudanar da bincike kan zargin bacewar N432bn.
Akwai alamun cewa hukumar na iya neman izinin kotu domin tsawaita tsare tsohon gwamnan don ba shi damar amsa ƙarin tambayoyi kan zargin almundahana.
Wani jami’in hukumar wanda ya buƙaci a sakaye sunansa, ya bayyana.cewa EFCC na duba yiwuwar samun izinin kotu bayan cikar sa'o'i 48 da.doka ta ba su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

