Shugaba Tinubu Ya Fito Ya Nemi Afuwar 'Yan Najeriya bayan Fara Azumi
- Mai girma Bola Tinubu ya halarci bude tafsirin Alkur'ani a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja
- Shugaba Tinubu ya yi jawabi a wajen Tafsirin, inda ya nuna muhimmancin da ke tattare da lokacin azumin watan Ramadan
- Hakazalika, Shugaban kasar ya kuma mika kokon bararsa ga 'yan Najeriya kan su yi masa afuwa idan ya aikata ba daidai ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika kokon bararsa ga 'yan Najeriya yayin da aka fara azumin watan Ramadan.
Mai girma Shugaba Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yafe masa idan har ya yi musu laifi a tsawon shekarun da ya yi a ofis.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaba Tinubu ya yi wannan roƙon ne ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026 yayin buɗe Tafsirin Alkur'ani mai girma na wannan shekarar da aka gudanar a masallacin fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Dokar zabe: Jam'iyyar ADC ta taso Tinubu a gaba, ta fadi shirin da take yi don hana magudi
Bola Tinubu ya yi magana kan azumi
Haka kuma, Tinubu ya yi magana kan haɗuwar watan azumin Ramadan da na Lent (wani azumin Kiristoci), inda ya ce hakan yana zama tunatarwa kan kyawawan ɗabi'u da dukkan addinan suka yi tarayya a kai.
“Azumin Ramadan ya zo daidai da na Lent, wanda hakan ke tunatar da mu kan kudurinmu guda na sadaukarwa, tarbiyya, addu’a, da kuma kame kai."
“Mun fara wannan Ramadan ne da dukkan koyarwar da yake ɗauke da ita gare mu baki ɗaya. Amma babban darasin shi ne kyautata wa mutane, yaɗa soyayya da imani, da kuma yafe wa juna. Ina cewa, idan na yi laifi, ku yafe mani a matsayinku na 'yan Najeriya.”
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya tunatar da 'yan Najeriya
Tinubu ya bayyana cewa ya kamata azumi ya wuce barin ci da sha kawai, ya ce dole ne ya zama alama ta nuna faffadar zuciya, yafiya, kyawawan ayyuka, da kuma son ɗan Adam, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Ya bukaci 'yan Nijeriya na kowane addini da su yi addu'ar neman zaman lafiya tare da ba da goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta'addanci, 'yan bindiga, da sauran matsalolin tsaro.
Tun da farko a cikin sakonsa ga Kiristoci da Musulmai, Shugaba Tinubu ya buƙaci mabiya addinan da su kasance kan-kan da kai a cikin ayyukansu ga Allah.
Shugaba Tinubu ya ce haɗuwar waɗannan lokuta biyu a rana guda yana tunatar da mu cewa a matsayinmu na mutane masu addini, muna da abubuwa da dama da muka yi tarayya a kai, kuma mu al’umma ɗaya ne a wajen Allah.

Source: Facebook
Babban limamin Aso Rock ya yi nasiha
Shi ma a nasa jawabin, babban limamin masallacin fadar shugaban kasa, Abdulwahid Suleiman, ya gode wa Allah SWT da ya nuna wa al'ummar Musulmi wani sabon lokacin azumi na Ramadan.
Limamin ya yaba wa salon shugabancin Tinubu tare da yin addu'ar neman lafiya, da karfi ga shugaban da tawagarsa, sannan ya roƙi Allah ya tabbatar da zaman lafiya da ci gaba ga dukkan 'yan Najeriya.
'Ban yafe ba'
Sahabi Abdulrahman ya bayyana cewa tabbas a yanzu dai bai yafewa shugaban kasar na Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: Shugaba Tinubu ya fadi dalilin sanya hannu a dokar zabe duk da korafe korafe
"Aa gaskiya ban yafe masa ba a yanzu dai, saboda bai nuna ya amsa kurakuransa ba. Ai ni dai yanzu ina ganin kawai zan iya yafe masa ne idan na ji an ce ya bar duniyar nan."
"Kamata ya yi ma ya yi murabus domin ya nuna alamun ba zai iya sauke nauyin da ke kansa ba."
- Sahabi Abdulrahman
Gwamna ya rage lokacin aiki saboda azumi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya saukakawa ma'aikatan gwamnati saboda shigowar watan azumin Ramadan.
Gwamna Nasir Idris ya amince da rage lokacin tashi daga wurin aiki domin ma'aikata su samu saukin gudanar da azumi.
A cikin sanarwar da aka fitar an bayyana cewa za a rika tashi daga wurin aiki da karfe 2:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Alhamis.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
