Ramadan: Kasashen da Za Su Yi Azumi Mai Tsawo da Mafi Karanci a Duniya a Ramadan

Ramadan: Kasashen da Za Su Yi Azumi Mai Tsawo da Mafi Karanci a Duniya a Ramadan

  • Al'ummar Musulmi sama da biliyan ɗaya sun fara azumin watan Ramadan na shekarar hijirar 1447 a faɗin duniya baki daya
  • Sa’o’in azumi a wasu kasashe za su ragu idan aka kwatanta da bara, inda ranar farko a wasu wurare za ta kai awa 12 da minti 46
  • Wasu kasashe kuma za su fi tsawon azumi, yayin da Brazil da Indonesia za su fi samun gajeren lokacin azumi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Fiye da al'ummar Musulmi biliyan ɗaya a duniya na suka fara azumin watan Ramadan na wannan shekara ta 2026.

Ramadan wata ce mai alfarma da ake gudanar da azumi, ibada da mayar da komai ga Allah Ubangiji Mahalicci SWT.

Yawan awanni da kasashe ke yi suna azumi
Mamba a kwamitin duban wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril da wasu Musulmai suna da salla Hoto: Simwal Usman Jibril, Mostapfa Alkharouf/Anadolu.
Source: Getty Images

Hasashen raguwar yawan awanin azumi a 2026

Ana sa ran sa’o’in azumi a shekarar 2026 za su ragu idan aka kwatanta da na bara, lamarin da zai kawo sauƙi ga masu ibada, cewar rahoton Khaleej Times na UAE.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

Saboda kalandar Hijira tana bin zagayowar wata, kowane wata yana da kwanaki 29 ko 30 gwargwadon ganin jinjirin wata.

Wannan sauyin na sa Ramadan yana matsawa gaba da kusan kwanaki 10 zuwa 12 a kowace shekara.

Bisa hasashen masana taurari, wasu kasashe sun fitar da sanarwar fara azumin Ramadan a ranar 19 ga Fabrairu 2026, sai dai sun ce za a iya farawa 18 idan an ga jinjirin wata

Har yau akwai kasashen duniya da ba su fara azumi ba
Masu duba jinjirin watan Ramadan a Saudiyya. Hoto: Inside the Haramain.
Source: Facebook

Yadda sa'o'in azumi ke bambanta a duniya

Sa’o’in azumi suna bambanta daga kasa zuwa kasa sakamakon bambancin yanayi da nisan kasa kamar yadda masana kimiyya suka tabbatar.

Musulmi na kaurace wa abinci, abin sha da bukatun jiki daga lokacin ketowar alfijir har faduwar rana a kowace rana.

A yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, sa’o’in azumi suna da matsakaicin tsawo saboda daidaiton hasken rana.

Kasashen da ke Arewa sosai suna da tsawon rana, wanda ke jawo karin tsawon sa’o’in azumi.

Awannin da kasashe ke yi suna azumi

Legit Hausa ta duba wasu kasashen da za su yi azumi na tsawon lokaci da sabanin haka a wannan wata na Ramadan.

Kara karanta wannan

Ramadan 2026: Fitar maniyyi da wasu abubuwa 6 da ke lalata azumi

Misali a Najeriya da ke yankin Yammcin Nahiyar Afirka, Musulmi suna yin azumi har na tsawon awanni 12 zuwa 13

Mazauna Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE za su yi azumin farko na kusan awa 12 da minti 46, kusan minti 30 kasa da na bara.

Yayin da watan ke ci gaba, sa’o’in azumi za su rika karuwa da ƴan mintuna kadan zuwa karshen watan.

A yankunan Arewacin Rasha, Greenland da Iceland, Musulmi za su fuskanci mafi tsawon azumi saboda tsawon hasken rana.

Kasashe kamar Norway, Sweden da Finland za su yi azumi sama da awa 16 a rana saboda tsawon yini.

A wasu sassan Sweden da Arewacin Canada, azumi na iya kaiwa har awa 20 saboda matsanancin hasken rana.

Malaman addini sun ba da damar bin jadawalin Makkah ko kuma na birni mafi kusa mai matsakaicin hasken rana.

Wsu kasashe za su fara azumin Ramadan a gobe Alhamis
Daya daga cikin mambobin kwamitin ganin wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril. Hoto: Simwal Usman Jibril.
Source: Facebook

Daya daga cikin mambobin kwamitin ganin wata daga fadar Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibril ya wallafa karin bayani game da yawan awannin azumi a wasu ƙasashe a shafinsa na Facebook.

Ya ce Musulmi a kasashen da ke kan ma’auni daga tsakiya kamar Indonesia da Malaysia za su yi azumi kusan awa 12 zuwa 14.

Kara karanta wannan

2026: Abubuwa 10 da ya kamata Musulmi ya sani kafin fara azumin watan Ramadan

Mafi karancin awanni da kasashe ke azumi

  • Brazil - awa 11 zuwa 13
  • Argentina - awa 11 zuwa 13
  • Afirka ta Kudu - awa 11 zuwa 13
  • New Zealand - awa 11 zuwa 13
  • Indonesia - 12 zuwa 14
  • Malaysia - awa 12 zuwa 14
  • Najeriya - awa 13 zuwa 14
  • Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE - awa 12 zuwa 13

Mafi yawan awanni da kasashe ke azumi

  • Norway - awa 16
  • Sweden - awa 16
  • Finland - awa 16
  • Sweden - awa 20
  • Canada - awa 20
  • Rasha - awa 20 zuwa sama

Kasashe da za a fara azumi ranar Alhamis

A wani labarin, kun ji cewa kasar Oman da wasu kasashen duniya uku sun tabbatar da cewa za a fara azumin watan Ramadana na shekarar 2026 a ranar Alhamis 19 ga watan Fabrairun 2026.

Hasashen masu ilimin taurari ya nuna cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Ramadan ba a ranar Talata a yawancin kasashen duniya.

Za a iya samun bambancin ranar fara azumi sakamakon hanyoyin da ake amfani da su wajen tabbatar da shigar wata a kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.