Ramadan: Kwankwaso Ya Tura Sako na Musamman ga Musulmin Najeriya da na Duniya

Ramadan: Kwankwaso Ya Tura Sako na Musamman ga Musulmin Najeriya da na Duniya

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bi sahun masu taya al'ummar musulmi barka da shigowar watan Ramadan
  • Kwankwaso ya yi fatan watan ya kara kusantar da kowane Musulmi ga Allah S.W.A, tare da samun farin ciki da kwanciyar hankali mai dorewa
  • Musulmin Najeriya sun fara azumin Ramadan ne a yau Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026 bayan fadar Sarkin musulmi ta sanar da ganin wata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya taya al’ummar Musulmi murnar fara watan azumin Ramadan mai alfarma.

Wannan sako na Kwankwaso na zuwa ne yayin da al'ummar musulmai a Najeriya suka dauki azumin farko na watan Ramadan yau Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan fara azumi, Shugaba Tinubu ya aika sako ga Musulmai da Kiristocin Najeriya

Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kwankwaso, tsohon dan takarar shugaban kasa ya aika sakon taya murna da fatan alheri ga daukacin musulmi a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Sakon Kwankwaso ga musulman Najeriya

A cikin saƙon mai cike da fatan alheri, Kwankwaso ya roƙi Allah da ya sanya watan mai tsarki ya zo da albarka da rahama ga Musulmi a faɗin Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Ya bayyana fatan cewa Ramadan zai cika zukatan muminai da natsuwa, ya kara kusantar da su zuwa ga Allah, ya tsarkake niyyarsu, tare da cika gidajensu da zaman lafiya da farin ciki.

"Ina yi wa dukkan al'ummar Musulmi fatan alheri da rahamar Allah yayin da suka shiga watan Ramadan mai alfarma.
“Allah Ya sanya wannan wata ya lullube zukatanmu da natsuwa, ya kusantar da mu zuwa gare Shi, ya tsarkake niyyarmu, ya kuma cika gidajenmu da zaman lafiya da farin ciki. Ramadan Mubarak,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Shehun Borno ya sanar da ganin watan Ramadan maimakon Sarkin Musulmi

Kwankwaso ya yi wa musulmai nasiha

Rahoton Leadership ya ce Kwankwaso ya kuma buƙaci Musulmi su yi amfani da wannan lokaci na azumi, sallah da nazari wajen ƙarfafa imaninsu, bunƙasa haɗin kai, tare da yawaita ayyukan alheri da taimako ga marasa galihu a cikin al’umma.

Kwankwaso.
Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wannan dai ya sa Kwankwaso ya shiga jerin manyan jagorori a Najeriya da suka fito suka taya musulmi murnar shigowar watan azumin Ramadan tare da fatan alheri.

Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, lokaci ne da Musulmi a faɗin duniya ke azumi, ibada da kara kusanci ha Allah Madaukakin Sarki.

Tinubu ya taya musulmi da kiristoci murna

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya musulmi da kiristocin Majeriya murnar fara ibadar azumi a lokaci guda.

Shugaba Tinubu ya bukaci su yi amfani da dama ta azumi da suka fara a rana guda a wannan shekara, a matsayin wata hanya ta samar da zaman lafiya, haɗin kai, da kwanciyar hankali a kasa.

Tinubu ya kara da cewa wannan abu ne da ke tunatar da mu cewa ’yan Najeriya na kowane addini suna da abubuwa da dama da suka yi tarayya a kai, kuma al’umma ɗaya ne a wajen Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262