Hakeem Baba Ahmed Ya Gano Abin da Yake Jefa El Rufai cikin Matsala
- Tsohon Mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi maganganu kan Nasir Ahmad El-Rufai
- Hakeem Baba-Ahmed ya soki tsohon gwamnan na jihar Kaduna kan yadda yake sakin baki yana maganganu
- Ya bayyana cewa ya kamata tsohon Ministan Abujan ya maida hankali ne wajen wanke kansa daga zargin cewa ya saci kudaden jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki Nasir El-Rufai.
Hakeem Baba-Ahmed ya soki tsohon gwamnan na Kaduna, kan matakan da yake ɗauka a daidai lokacin da yake fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Source: Twitter
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne ranar Talata, 17 ga watan Fabrairun 2026 yayin shirin ‘Political Paradigm’ a tashar Channels Tv.
Me Hakeem Baba-Ahmed ya ce kan El-Rufai?
Tsohon mai ba mataimakin shugaban kasar shawara ya bayyana cewa Nasir El-Rufai mutum ne mara daukar shawara.
“Abin takaici, Malam Nasiru a dabi’ance mutum ne mara daukar shawara. Domin da yana jin shawara, na tabbata a wani guri za a samu wanda zai ce masa, ‘yi ƙoƙari ka rage abubuwan da ka ke yi’."
"Wannan gwamnati ce da ba ta ɗaga ƙafa. Suna zarginsa ne, kuma suna kokarin gabatar da hujjoji a gaban alkali cewa lokacin da yake kan mulki, Malam Nasir El-Rufai ya karkatar da kuɗi kuma ya sace kuɗi.”
- Hakeem Baba-Ahmed
Hakeem ya ce El-Rufai ya takalo fada
Ya kara da cewa tun farko El-Rufai yana fuskantar zarge-zargen cin hanci ne kawai, amma sai tsohon ministan ya fito a gidan talabijin yana yin wasu kalamai da ke nuna cewa shi ko wani da ya sani yana da hannu a ayyukan da ba sa kan ka’ida.
“Sannan yanzu kuma ka rubuta wasika da sa hannunka, kana neman mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya yi bayani kan shigo da wasu sinadarai masu haɗari a cikin kasarsa.”
- Hakeem Baba-Ahmed

Source: Twitter
Wace shawara ya ba El-Rufai?
Da aka tambaye shi ko ya kamata El-Rufai ya guji rubuta wa NSA wasika, Hakeem Baba-Ahmed ya ce da shi ne zai ba shi shawarar ya kame kansa.
“Ina nufin da ni ne nake ba Nasir shawara a cikin wannan mawuyacin hali, da na ce masa: Na ɗaya, kai babban mamba ne a jam’iyyar ADC."
"Za ka fi amfani ga ADC idan kana yawo a matsayin mutum mara kashi a gindinsa, ba wanda zarge-zarge da faɗace-faɗace suka yi wa katutu ba."
“Akwai fage kaɗan da za ka iya yin faɗa a kansu. Don haka yi ƙoƙari ka takaita ɓarnar. Mayar da hankalinka wajen wanke kanka daga zargin cewa ka sace kuɗin al’ummar jihar Kaduna."
“Amma ga shi nan ba a ba shi wannan shawarar ba, ko kuma shi ne ba ya son ta. Yanzu kuma (gwamnati) tana cewa muna da maganganu guda uku a kanka."
- Hakeem Baba-Ahmed
Binciken da EFCC ke yi kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Majiyoyi sun bayyana cewa EFCC na bincikar tsohon gwamnan ne kan zargin karkatar da kudaden jihar Kaduna da ya yi mulkin shekaru takwas.
Hakazalika, an bayyana cewa jami'an hukumar yaki da rashin gaskiyar na bincikar El-Rufai kan zargin daukar nauyin ayyukan ta'addanci.
Asali: Legit.ng


