An Yi Zanga Zangar Korar 'Yan Arewa a Rivers, an Fasa Shaguna da Lalata Dukiya

An Yi Zanga Zangar Korar 'Yan Arewa a Rivers, an Fasa Shaguna da Lalata Dukiya

  • Wasu mazauna jihar Rivers sun yi zanga-zangar adawa da zaman 'yan Arewa suna bukatar su bar garin, inda suka lalata dukiyar miliyoyin Naira
  • Shugaban 'yan Arewa mazauna Rivers ya fito ya yi bayani game da abin da ya faru tare da kira ga hukumomi su dauki matakin da ya dace
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta yi karin haske game da lamarin tare da tabbatar da cewa ta kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da jawo rigimar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - An lalata kayayyaki da darajarsu ta kai daruruwan miliyoyin Naira sakamakon zanga-zangar da aka yi kan ’yan Arewa a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.

Ana zargin cewa wani dan asalin Igwuruta, Samuel Festus da aka zarga da satar babur daga wani shago mallakin ’yan Arewa ya mutu a ƙoƙarin kwato babur ɗin, an ce an daba masa wuka, kuma daga bisani ya rasu.

Kara karanta wannan

Trump ya jero sunayen 'yan Najeriya da ya kwace kadarorinsu a Amurka

Yadda aka yi zanga zangar adawa da Hausawa
Masu zanga-zangar adawa da Hausawa a Rivers. Hoto: @arhermadd
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin da ya faru a ranar 10 ga Fabrairu ya haddasa zanga-zanga, inda matasa suka yi zargin cewa masu acaba daga Arewa ne ke da alhakin mutuwar Festus.

Zanga zangar korar 'yan Arewa

Rikicin ya tsananta yayin da matasa suka toshe hanyar Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Fatakwal, suna neman a haramta aikin 'yan acaba da suka fito daga Arewa a yankin.

Sun kuma nemi a rufe wuraren tara tsofaffin karafa da ake zargin ’yan Arewa ke sarrafawa, a kama su tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a kisan Festus, sannan makiyaya su bar yankin.

Masu zanga-zangar sun bai wa hukumomin tsaro wa’adin sa’o’i 48, suna gargadin cewa idan ba a biya buƙatunsu ba, al’umma za ta ɗauki mataki.

Tashin hankalin ya ƙara muni a ranar Asabar lokacin da wani mai suna Zakara Afaaruwu ya daba wa wani ɗan kasuwa daga Jihar Benue, Higightor Wenem, wuka har lahira yayin takaddama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

Lamarin ya sake tayar da hankula, inda aka kai sabbin hare-hare kan ’yan kasuwar Arewa a Igwuruta, aka lalata tare da wawushe shaguna da dama.

Bidiyon wani sashe na zanga-zangar:

Maganar shugaban Hausawan Rivers

Shugaban kungiyar Hausawa a Jihar Rivers, Malam Musa Saidu, ya bayyana matuƙar alhini kan kashe-kashen, tare da yin gargaɗi kan danganta aikata laifi da al’ummar Hausawa ko wata ƙabila.

Ya ce:

“An samu saɓani tsakanin wani matashi ɗan Arewa da wani ɗan asalin Igwuruta, wanda abin takaici ya kai ga mutuwa.
"Bisa bayanan da na samu, domin ban je wurin da kaina ba, ana zargin matashin ɗan Arewa ya daba masa wuka, ya rasu. Hakan ya jawo zanga-zanga, amma abin da ake cewa shi ne Hausawa su bar yankin.
"Idan wani ya aikata laifi, aikin hukumomin tsaro ne su kama shi su gurfanar da shi bisa dokar ƙasa. Me ya sa za a riƙa zanga-zanga ana cewa Hausawa su tafi?
“Tuni akwai ƙiyayya mai tsanani kan ’yan Arewa. Idan za a tuna, a lokacin zanga-zangar #EndSARS, an ruwaito cewa sama da ’yan Arewa 100 aka kashe a yankin Oyigbo.

Kara karanta wannan

Ana ruguza allunan tallata Tinubu a Zamfara, ran jam'iyyar APC ya baci

Taswirar jihar Rivers
Taswirar jihar Rivers a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Rivers ta tabbatar da kama wanda ake zargi da hannu a daba wukar da ta yi sanadin mutuwa a Kasuwar Oil Mill, tana mai cewa yana tsare yayin da bincike ke ci gaba.

'Yan ta'adda sun raba wasiku a Kwara

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu kauyuka a jihar Kwara sun sanar da cewa 'yan ta'adda sun raba wasiku da cewa za su kai musu hari.

A cikin wasikar, 'yan ta'addan sun bayyyana cewa za su kashe mutane ba kakkautawa domin babu abin da suka kware a kai kamar kisa.

Sarkin wani yankin da aka aikawa wasika ya sanar da jami'an tsaro, inda aka bayyana cewa an samu karin sojoji da ke sintiri a yankunan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng