Ramadan: Tagomashin da Gwamna Abba Ya Yi Wa Mutanen Kano saboda Azumi
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon kayan azumi domin saukakawa mutane a lokacin watan Ramadan
- Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin raba buhunan shinkafa ga dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano
- Gwamnan ya kuma kafa kwamitoci da su sanya ido tare da tabbatar da cewa an yi rabon shinkafar yadda ya kamata ba tare da rashin gaskiya ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da raba buhunan shinkafa guda 54,600 domin rage raɗaɗin matsin rayuwa da mazauna jihar Kano ke fuskanta a lokacin watan Ramadan.
Bikin kaddamarwar, wanda aka gudanar ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairun 2026 a titin Maganda da ke Kano, ya nuna farkon shirin tallafin Ramadan na shekara-shekara.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook.
Gwamna Abba ya kaddamar da rabon tallafi
Gwamnan ya bayyana aikin a matsayin tsohuwar al’ada ta kowace shekara da nufin taimaka wa gajiyayyu a lokacin watan alfarma.
Yayin da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa:
“Abin alfahari ne da daraja a gare ni kasancewa tare da ku a yau domin ƙaddamar da raba tallafin Ramadan na shekarar 1447 bayan hijira.”
Ya bayyana cewa wannan tallafin zai karade daukacin kananan hukumomi 44 na jihar da ma sauran rukunin mutanen da aka zaɓa za su amfana.
Buhuna nawa za a raba?
A cewarsa, jimillar manyan motocin shinkafa guda 91, waɗanda suka yi daidai da buhu 54,600 masu nauyin kilogiram 50, za a raba a faɗin jihar.
Daga cikin wannan adadi za a raba motoci 44 kai tsaye ga ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Sauran motoci 47 kuma za a raba su ga kungiyoyi da daidaikun mutanen da aka zaɓa domin tallafa musu a lokacin azumi.

Kara karanta wannan
Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau
Gwamna Abba ya kafa kwamitoci
Domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, gwamnan ya sanar da kafa kwamitoci a matakin jiha da na kananan hukumomi domin sanya ido kan samarwa, rabawa, da kuma isar da shinkafar ga waɗanda suka dace.

Source: Facebook
“A matakin jiha, sakataren gwamnatin jiha ne zai jagoranci kwamitin, yayin da ma’aikatar noma za ta kasance mai daidaita ayyukan."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Daga karshe, gwamnan ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki, gami da gwamnatin tarayya da sauran masu hannu da shuni, da su ba da tasu gudunmawar domin sauƙaƙa wa al’umma matsin tattalin arziki a lokacin Ramadan.
Tinubu zai tarbi Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tarbi Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai isa Kano ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026 domin karbar Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zuwa jam’iyyar APC.
Hakazalika, an tsara cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamnonin APC da dama za su halarci taron na tarbar gwamnan
Asali: Legit.ng
